Mutane 6 mafi arziki a arewacin Najeriya
Mun tattaro muku mutane 6 mafi arziki a Najeriya da labaran arzikinsu, ga jerin sunayen su nan bisa ga binciken da aka gudanar. A sha karatu lafiya:
1. Alhaji Aliko Dangote
A matsayin na mafi arzikin kudi na Afirka gaba daya game da cewar mujallar Forbes. A shekarar 2014, shine mutum na 23 mafi arziki a fadin duniya.
Aliko Dangote na da kimanin arziki $21.5 Billion.
2. Theophilus Danjuma
Janar Theophilus Yakubu Danjuma (GCON, FSS, psc) tsohon soja ne, dan siyasa, kuma dan kasuwa. Ya kasance babban hafsan sojan Najeriya tsakani shekarar 1975 zuwa 1979. Kuma ya zama ministan tsaro karkashin mulkin Obasanjo. Shine shugaban kamfanin man fetur South Atlantic Petroleum (SAPETRO).
3. Abdulsamad Isyaku Rabiu
AbdulSamad Isyaku Rabiu (CON) wani hamshakin maikudi ne kuma dan kasuwa. Shine shugaban BUA group, wata kamfani mai sayar da komai kuma arzikinshi ya kai $2.5 billion.
A shekarar 2013, ya shiga jerin masu kudin duniya.
4. Mohammed Indimi
Mohammed Indimi shine shugaban kamfanin Oriental Energy Resources, masu rijiyoyin man fetur. Ya kafa wannan kamfanin a shekarar 1990, sunada rijiyoyin mai Ebok Field (OML 67), Okwok Field (OML 67, and OML 115).
5. Alhaji Sayyu Dantata: MRS Group
6. Umaru Abdul Mutallab, tsohon shugaban First Bank kuma Shugaban Jaiz Bank
https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=br_tf#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng