Wata musulma ta fitar da kiristoci daga gidan yari, ta basu kudin motar komawa gida
A kokarin ganin an tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a tsakanin addinai da kuma fahimtar juna mai dorewa tsakanin kungiyoyi da addinai a Nijeriya, wata mata Musulma ta ’yantar da wasu kiristoci daga gidan yarin Kaduna, domin su samu daman gudanar da ibadarsu ta azumin kwanaki 40 da Kiristocin suke yi duk shekara.
Cikin jawabinta a lokacin wannan bikin ’yantarwa, wacce ta dauki wannan dawainiya, Hajiya Ramatu Tijjani ta bayyana cewa ‘Lenten,’ lokaci ne na musamman kuma mai daraja a wurin mabiya addinin kiristanci mabiya mazhabar Katolika, don haka Nijeriya na matukar bukatar addu’o’i daga dukkan ‘yan kasa domin a samu a fita daga kangin da ake ciki. Inda ta ce bisa wannan ne ya sa ta yi belin kiristocinn daga gidan yari don su samu cikakkiyar daman zuwa iklisiyya da kuma yin addu’o’i a tare da ‘yan uwansu da abokan arziki.
KU KARANTA: An gano gidan buga kudi a jihar Kebbi
Bayan amsar belin, Hajiya Ramatu ta kuma ba wadannan kiristci kudin motar da za su koma gida wurin iyalansu.
Daya daga cikin wadanda suka samu wannan beli, Mista Yakubu Musa dan shekaru 45 da haihuwa, , wanda kuma ya shafe makwanni uku ne a gidan yari saboda tarar N6000, ya bayyana irin farin cikin da ya tsinci kansa a sakamakon wannan beli nasa da aka yi.
Ya ce yanzu zai tafi gida inda zai samu Iyalansa domin mu gudanar da Ibadar azumin kwanaki 40 tare. Sannan kuma ya ce daga wannan lokaci zai sauya halayyansa zuwa kyawawa. Kuma ya yi kira ga wadanda ke cikin gidan yarin da su ci gaba da yi wa kasa addu’a.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng