Bayan dawowar Buhari, sojin saman Najeriya sun kai samame dajin Sambisa, sun yi gagarumar nasara
Sojojin saman Najeriya sun bada sanarwar kai samame a dajin Sambisa bisa ga wasu bayanan leken asiri da suka samu dake cewa wasu 'yan Boko Haram suna nan boye a dajin kuma suna da rumbun makamai.
Majiyar mu ta nemi karin bayani daga kakain hedkwatar sojojin mayakan sama dake Abuja Group Captain Ayodele Fagbowiwa.
Kakakin yace sun kai farmaki a dajin Sambisa inda jirgin leken asiri ke shawagi. Yace tun farkon wannan shekarar rundunarsu ta sabunta duk sintirin da yankunansu su keyi inda ake yakin a matsayin rigakafi domin kada 'yan burnushin 'yan Boko Haram din da suka rage a raye su sake haduwa wuri guda suyi ta'adanci.
KU KARANTA: Darajar Naira ta fadi dalilin dawowar Buhari?
Yace a wannan karon jirginsu na leken asiri dake sintiri a dajin ya hango wata motar 'yan ta'adda tana kutsawa cikin wani sarkakin duhu a dajin. Jirgin ya dinga binsu cikin siri har ya ga inda suka shiga inda nan take ya sanarda mayakan da suka dinga sako bamabamai daga sama. Sanadiyar bamabaman sojojin sun dinga jin karar fashewar abubuwa da ake kyautata zaton makamai ne da man fetur.
Air Commodor Ahmed Tijjani Baba Gamawa yace idan an duba dajin Sambisa ba karamin jeji ba ne wanda yake da sarkakiya amma saboda kwarewar sojojin da kayan aiki suka iya farma wurin. Wannan nuni ne cewa sojojin saman sun samu nasarar ruguza rumbun makaman 'yan Boko Haram.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng