Shugaban ƙungiyar ta’addanci ‘Al-Shabab’ ya miƙa wuya ga gwamnatin ƙasar Somalia

Shugaban ƙungiyar ta’addanci ‘Al-Shabab’ ya miƙa wuya ga gwamnatin ƙasar Somalia

Dakarun sojojin kungiyar kasashen Afirka dake gudanar da aikin tsaro na musamman, AMISOM sun tabbatar a ranar Alhamis cewa shugaban kungiyar yan ta’adda ta Al-Shabab Hussein Mukhtar mai lakabi da Abu Mansur ya mika wuya ga dakarunta dake garin Baidoa a kasar Somalia.

Shugaban ƙungiyar ta’addanci ‘Al-Shabab’ ya miƙa wuya ga gwamnatin ƙasar Somalia
Shugaban ƙungiyar ta’addanci ‘Al-Shabab’ ya miƙa wuya ga gwamnatin ƙasar Somalia

Dakarun AU, suna kira ga sauran mayakan Al-Shabab dasu ribaci tayin afuwar da gwamnati tayi musu kamar yadda Dakarun suka sanar cikin wata sanarwar, inda suka bukace su dasu ajiye makamansu, tare da hada kai da sauran al’ummar kasar Somalia wajen sake gina kasar Somalia.

Sanarwar ta cigaba da fadin: “AMISOM na fatan duk sauran maza da mata yan kasar Somalia da suka shiga ta’addanci zasu yi koyi da halin Mukhtar.”

Shugaban ƙungiyar ta’addanci ‘Al-Shabab’ ya miƙa wuya ga gwamnatin ƙasar Somalia
Shugaban ƙungiyar ta’addanci ‘Al-Shabab’ a hagu

KU KARANTA: Yan bindiga sun buɗe wuta a gidan Olisa Metuh dake Abuja

Tun a shekarar 2014 ne dai gwamnatin kasar Somalia ta sanar da tayin afuwa ga duk wani dan ta’ddan daya ajiye makami ya mika wuya.

Shugaban ƙungiyar ta’addanci ‘Al-Shabab’ ya miƙa wuya ga gwamnatin ƙasar Somalia
Shugaban ƙungiyar ta’addanci ‘Al-Shabab’ ya miƙa wuya ga gwamnatin ƙasar Somalia

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito cewa kungiyar Al’Shabab ta mamaye kudanci da yankin tsakiya na kasar Somalia, tare da sanya tsauraran dokoki ga jama’an yankin, kamar su hana jin waka, har ma da yanke ma barayi hannu.

Duk da cewa sojojin gwamnatin kasar dana AU sun samu nasarar kwato yawancin yankunan, amam fa yan’ta’ddan suna kai musu harin mummuke, inda suka karkashe yan majalisun kasar da dama, har ma suka kai hari fadar shugaban kasa.

Shugaban ƙungiyar ta’addanci ‘Al-Shabab’ ya miƙa wuya ga gwamnatin ƙasar Somalia
Shugaban ƙasar Somalia

Tayin afuwan da gwamnatin kasar Somali tayi ma kungiyar Al-Shabab ya biyo bayan hallaka babban shugabansu Ahmed Godane da kasar Amurka tayi ta amfani da ruwan bamabamai. Kuma tun bayan mutuwar Godane ne sai kawunan yayan kungiyar ta rabu, amma duk da haka, basu daina kai hare hare ba.

Yayin da yake jawabi, shugaban kasar Hassan Mohamud yace ya san abinda ya shigar da mutane da dama kungiyar Al-Shabab, ciki har da talaucin kudi, da kuma masu ganin suna aikin Allah ne.

Shugaba Mohamud ya kara da cewa ya san wasu jama’an kasar basu ji dadin matakin bayar da afuwa ga yan ta’addan ba, amma yace: “Kuyi hakuri, ku amshe su, kuma ku gafarta musu, don mu samu cigaba tare da mantawa da abin daya faru a baya.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel