Fari: Yunwa ta kashe mutane 110 a wannan kasa cikin sa’oi 48
Kamfanin Dillancin Labarun ya kalato shugaban kasar Somaliya inda ya sanar da mutuwar mutane 110 saboda yunwa.
shugaban na Somaliya Khairi da ya fitar da bayani a ranar asabar ya fadi cewa; Mutanen da su ka mutu sun rika yin gudawa mai tsanani, a yankin kudancin kasar.
Ya ci gaba da cewa; Wajibi ne ga mutane kasar ta Somaliya a duk inda su ke da su taimakawa ‘yan’uwansu ‘yan kasar mabukata da su ke fama da yunwa.
KU KARANTA: Daki daki, alƙalumman ɓarnar da Boko Haram suka yi jihar Borno
Har ila yau, shugaba ya ci gaba da cewa; “Aikin da ke gaban hukuma shi ne taimakawa mutanen da fama da yunwar, saboda farin da kasar ta ke fama da shi.”
A yankin al-Bay na kasar mahukunta sun sanar da mutuwar mutane 69 mafi yawancinsu kananan yara da tsofaffi.
Tun a karshen watan Febrairu ne dai gwamnatin kasar ta Somaliya ta sanar da halin ko ta kwana saboda fari mai hatsari da kasar ta ke fama da shi.
Mutane miliya 3 ne dai farin ya jefa cikin yunwa kamar yadda kungiyoyin fararen hula su ka ambata.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng