Ra’ayi: Dalilin daya sa yan shi’a basa son birnin Makkah

Ra’ayi: Dalilin daya sa yan shi’a basa son birnin Makkah

Abu Adnaan wani ma’abocin aiko da sakkonni ne zuwa ga Legit.ng, a wannan karon ya aiko mana kasida kan baiwa dakin Allah wato Ka’abah.

A matsayin Ka’abah, tun kafin haihuwa manzon Allah Annabi Muhammad (S.A.W) an samu wani Sarkin Habasha mai suna Abraha Al-Hashram wanda yayi kokarin rusa dakin Ka’abah saboda yana bakin ciki da yadda mutane daga ko ina a duk fadin duniya suke tururuwar zuwa yin bauta a gidan Annabi Ibrahim, kamar yadda ake kiran Ka’abah a wancan lokaci.

Ra’ayi: Dalilin daya sa yan shi’a basa son birnin Makkah
Ra’ayi: Dalilin daya sa yan shi’a basa son birnin Makkah

Saboda haka en Al-Hashram ya gina wata katafaren cocin daya fi girma a duniya, manufarsa kuwa itace karkatar da hankulan mutane daga daina zuwa ziyara dakin Ka’abah dake Makkah, su koma zuwa cocinsa dake Habasha.

Hakan ya bakanta ma wasu mutanen Makkah rai, sai suka tafi cocin suka rusa wani bangarensa, wanda sanadiyyar haka Sarki Abraha ya yanke shawaran daukan fansa ta hanyar rusa dakin Ka’abah. Sarki Abraha ya shirya sojoji dubu ar’ba’in da manyan giwaye da zasu rugurguza Ka’abah, a wancan zamani kuwa, yan kabilar Annabi, wato Quraish sune suke daukan nauyin kula da Ka’abah.

KU KARANTA: Likitoci sun ceto rayuwar wani Kunkuru ta hanyar tiyatan sulalla

Yayin da Quraishawa suka samu labarin shirin, sai suka razana, amma daga cikinsu sai aka samuw ani jarumi mai suna Nufail ibn Habeeb, wanda ya shirya wata karamar runduna da zata kare Ka’abah, amma sai rundunar Sarki Abraha tafi karfinsa, kuma suka kama shi.

Ra’ayi: Dalilin daya sa yan shi’a basa son birnin Makkah
Ra’ayi: Dalilin daya sa yan shi’a basa son birnin Makkah

Da mutanen Makkah suka fahimci babu yadda suka iya da rundunar sarki Abraha, sai suka roki Abraha da cewa zasu bashi kashi daya bisa ukun duk kayan gonakinsu, don ya kyale Ka’abah, amma ya ki. Daga nan sai kawai suka kwashe kayayyakinsu suka koma bayan duwatsu can nesa da gari.

Yayin da rundunar Abraha suke shirin shigowa cikin garin Makkah, sai Nufail ya gudo, shima ya ruga zuwa ga mutanensa a inda suke boye, babu yadda zasu yi da Abraha.

Cikin ikon Allah sai ga wasu tsuntsaye sun sauko daga sama, kowannensu dauke da duwatsun wuta guda uku, daya a baki biyu a kafafu, suna jifan mayakan sarki Abraha dasu, da dama daga cikin mayakansa Abraha sun mutu murus.

Sai dai abin mamaki a yau shine yadda wasu mutane masu kiransu musulmai suke nuna kiyayya ga birnin Makkah, idan Allah ya halakar da mutanen Abraha a zamanin Jahiliyya, me zai faru da na wannan zamanin?

Muddin yaji baya son garin Makkah, toh ya duba imaninsa, don tantance sahihancin musuluncinsa, idan malaman kasar ne baka so, toh ka yi karatu. Idan kana sukan mutanen kasar, toh ka sake tunani don kuwa ka fara bin hanyar yan bidi’a, idan kana cin zarafin malaman Makkah toh kayi tunani don wata kila ka fara daukan ra’ayin yan shi’a.

Idan kana sukan dokokin garin Makkah, duba da kyau domin ka fara yin halayyan jama’an Ahmad Ghulam shugaban Ahmadiyya, idan kana zagin akidar Makkah, kai ma sake tunani don kuwa ka fara daukan halayyan yan Boko Haram, ISIS da sauransu.

Idan kuwa kana kin tsarin mulkinsa, wata kila kai munafiki ne, idan kana zagin shugabanninta, tabbasa ka saki layin Sunnah, idan kuwa ka saki Sunnah toh tabbas baka son Annabi, idan kuwa haka ne, ta yaya za’a kira Musulmi?

Idan kana yin shagube ga dakin Allah, ka duba kwakwalwar ka, wata kila cut ace ke damunka tun kafin kasa ta hadiye ka.

Wannan kasida ra’ayin marubucin ne ba ra’ayin Legit.ng bane, muna gayyatar duk masu aiko da hotuna da kasidu. Zaka iya aiko mana da abinda kake sha’awar rubutu a kai da karin bayani a kanka ta Blogger@corp.legit.ng.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng