Rikicin makiyaya zai iya jawo babban barazana ga hadin kai Nijeriya – Inji shugabanin kirista
Shugabanin kungiyar kiristoci ta Najeriya sun jaddada cewa rikicin makiyaya a sasan kasa ya fi ta’addancin ‘yan Boko Haram barazana ga hadin kan Najeriya.
Shugabannin Kirista sun furta cewa mafi girman barazana ga hadin kan Najeriya yanzu ba Boko Haram ba ne, amma rikicin Fulani makiyaya da suke kashe 'yan Najeriya a sassa daban daban na kasar.
A wani taron kara wa juna ilmi na cocin katolika, Catholic Bishops Conference of Nigeria (CBCN) a ranar Lahadi, 5 ga watan Maris a birnin Abuja, shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Rev. Samson Ayokunle, shugaban CBCN, fasto Ignatius Kaigama da kuma fasto na cocin Anglican ta tarayya, fasto Nicholas Okoh sun kira gwamnatin tarayya da babban murya domin kirkiro kwakwarar matakai na magance rikicin Fulani makiyaya.
KU KARANTA KUMA: Sakona na Tuwita a shekarar 2012 ba don ya haifar da tashin hankali na yi shi ba
shugaban CBCN, fasto Ignatius Kaigama ya musanta kalaman wasu 'yan Nijeriya cewa addu’o’i kawai ke iya warware matsalolin Nijeriya, ya ce ko da shike kasar na bukatar addu’a, amma ya kamata gwamnati ta daura aniyan durkuce makiyaya yanda ta yi da ‘yan Boko Haram.
Fasto Nicholas Okoh ya gayawa jami'an gwamnati da suka halarci taron sun sanar da gwamnatin cewa 'yan Nijeriya ba su yi farin ciki da wannan al’amari.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng