Fasto Suleiman, abokin rikicin gwamna El-Rufai ya danƙara ma wata mata ciki
An yi karar babban faston cocin Omega of Fire dake garin Auchi na jihar Edo, Fasto Suleman kan zarginsa da wata mata mai suna Stephanie Otobo tayi na cewa ya dankara mata ciki, ya kuma yaudareta bayan yayi mata alkawarin aure, sa’annan yana amfani da yansanda wajen cin zarafinta.
Ita dai Stephanie mawakiya ce mazauniyar kasar Canada, ta shigar da kara ne ga babban sufeton yansanda na kasa ta hannun lauyan ta, fitaccen lauya Festus Keyamo, inda ta bayyana ma Sufeton yansanda cewa Fasto Suleiman ya sa yansanda sun kamata a ranar 3 ga watan Maris a bankin UBA, inda har yanzu tana hannunsu, ba tare da an bata ko abinci ba.
Lauya Festus Keyamo ya bayyana cewa a watan Satumbar 2016 ne Stephanie ta hadu da Fasto Suleiman, inda ya bayyana mata ya saki matarsa, do haka yana muradin aurenta don ta haifa masa yaya maza, da haka suka fara soyayya har ya kai kudin gaisuwa.
KU KARANTA: Ta fatattaki mijinta bayan kwashe shekaru 6 ba tare da ya biyata sadakin aure ba
Sakamakon haka ya sanya Stephanie yin watsi da harkarta na waka, ta kuma baro kasar Canada ta dawo Najeriya suka cigaba da soyayya da Faston, sai dai bayan Farkar Faston ta smau ciki ne sai Faston ya nuna bacin ransa, saboda yana tsoron kada abin ya fita ga jama’a musamman mambobin cocinsa.
Daga nan sai yayi kokarin ta zubar da cikin, amma taki, daga baya ya samu nasarar bata wani jiko, inda ta dinga zubar da jini har cikin nata ya zube, faruwar haka ya sanya Stephanie tserewa daga fasto Suleiman, ta koma garin Warri inda ta bayyana ma wani Faston labarin tsakaninta da Fasto Suleiman.
Daga bisani Fasto Suleiman ya bita kasar Canada ya bata hakuri, tare da neman afuwanta, sai ya roke ta data dawo Najeriya, inda a satin daya gabata ne ta dawo Najeriya, dawowarta ke da wuya Faston ya hada baki da yansanda, wadanda suka kamata a farfajiyar banki.
Sai dai Stephanie ta shaida ma Fasto Suleiman ta bakin Lauyan ta cewa tana da hotunan tsirara haihuwar uwarsa, kuma zata sake su a yanar gizo. Amma duk da haka, Faston yaki amincewa ta auri Stephanie.
Ita kuma Stephanie ta bukaci Faston ya biya ta naira miliyan 500 saboda bata mata lokaci da yayi ba tare da ya aureta ba, sa’annan ta bukaci daya daina yin barazana ga rayuwarta, da cin zarafinta. Daga karshe lauyanta ya baiwa Faston kwanaki 7 daya biya kudaden ko kuma su kai shi gaban kuliya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng