Wata mata mai yara 6 ta yar da yaro a tsalanga

Wata mata mai yara 6 ta yar da yaro a tsalanga

- Da gudu aka kai yaron baban asibiti na Abubakar Tafawa domin duba lafiyan shi

- Matar da mai suna James ta ce ta yar da yaron ne domin rashin wadata

- Mijin yana asibiti wajen jinya, bamu da abinci da zamu ci, muna mutuwar domin yunwa

An kama wata mata da ta yar da yaro a cikin rami domin talauci a jihar Bauchi. Matan ta yi kuka a baban tasha na yan sanda a ranar Juma’a suka nuna ta ma mutane.

Kukan jariri ne maƙwafta su ka ji suka kuɓutar da shi bayan ya yi wajen sa’o’i 12 a cikin ramin.

KU KARANTA: An damke wani mai taimakawa wajen garkuwa da mutane

Da gudu aka kai yaron baban asibitin Abubakar Tafawa domin duba lafiyan shi. Matar mai suna James ta ce ta yar da yaron ne domin rashin wadata bayan mijin ta ya rasa aiki da kuma yanayin tattalin arziki na kasar Najeriya.

Ta ce: “Abubuwar sun yi tsanani, miji na bai da aiki, ya yi hatsari wata uku da suka wuce ya kuma damun mutuntakan shi. Mijin yana asibiti wajen jinya, bamu da abinci da zamu ci, muna mutuwar domin yunwa. Na haifu a gida ne sai na yar da yaron a tsalanga domin ban san yar da zan kula da shi. Ban gayawa miji na ba dai.”

Kwamishiona yan sanda na jihar, Zaki Ahmed, ya ce ana kan binciken al'amarin amma an kai yaron waje yan kula da mutane acikin asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel