Adadin musulman duniya zai tserewa na Kiristoci cikin shekaru 53
- Bincike ta nuna cewa addinin musulunci ne addinin da tafi cigaba a fadin duniya musamman a tuari da Amurka ta yamma
- Cibiyar Pew Research Center tayi ikirarin cewa cikin shekaru 53 masu zuwa, adadin musulmai zai tserewa na kiristoci
- Game da binciken, musulmai sunfi hayayyafa wanda shine daya daga cikin dalilan yawan
Bincike ya nuna cewa har yanzu adadin kiristocin duniya yafi na musulmai. Amma cikin shekaru 53 daga yau, masu bincike suna bada tabbacin cewa yawan mabiya addinin Islama zai tserewa na Kiristoci.
Game da cewar cibiyar Pew Research Center dake zauna a birnin Washington DC, addinin musulunci ce addini mafi cigaba a yanzu kuma zata cimma na kiristoci a shekarar 2070.
KU KARANTA: Jonathan zai sasanta rikicin PDP
Daya daga cikin dalilan shine musulmai suna gudun hijra zuwa nahiyoyi musaman Amurka ta yamma da Turai.
Bugu da kari, kashi 62 cikin 100 na musulmai na zaune a nahiyar Asiya kuma musulmai sun fi yawa a kasashen India, Indonesia, Pakistan, Bangladesh, Iran and Turkey.
A kasar 2010, akwai musulmai 1.6 billion a duniya, wanda shine kasha 23 cikin 100 na mutanen duniya. Kuma kiristoci na da yawan 2.2 billion.
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng