Darussa 5 daga rayuwar korarriya yar Fim, Rahama Sadau
A ranar Lahadi 2 ga watan Oktoba ne dai kungiyar yan Fim na kasa ta dakatar da shahararriyar yar Fim din Hausa mai suna Rahama Sadau saboda ta rungumi wani mawakin hausa mai suna ClassiQ a cikin wata wakarsa.
Dalilin wannan runguma ne dai kungiyar ta sallame ta daga harkar fim gabaki daya, saboda ta karya dokar kungiyar na hana kusanci da maza.
Sai dai jim kadan bayan an dakatar da ita ne, sai wasu furodusoshin finanan turanci suka nemi su yi aiki tare da ita cikin fina finansu, inda a ranar 8 ga watan Oktoba na shekarar 2016 ta fito a cikin wani Fim na kamfanin EbonyLife Tv.
KU KARANTA: Aisha Buhari ta ƙaddamar da Asibitin tafi-da-gidanka don sauƙaƙa ma talakawa
Bugu da kari a ranar 15 ga watan Oktoba ta sanar da samun gayyata daga fitaccen mawakin duniya mai suna Akon inda ya gayyace ta kamfanin fim din Hollywood.
Cikin wannan sallam da Rahama tayi fama da shim un zabo muku darussa 5:
1. idan wata kofar ta kulle maka, wata zata bude maka
2. Samun kalubale a rayuwa alamu ne na samun nasara a gaba
3. Idan mutane sun zarge ka, kada kayi kasa a gwiwa wajen yin bayani
4. A duk abinda kasa a gaba, sa’a na tare da kai, kai dai cigaba da nema
5. Idan baka wahala ba, ba zaka darajta abin da ka cimmawa ba
Ga bidiyon daya sa aka dakatar da Rahama Sadau
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng