Jami’an EFCC sun kai samame gidan Abdullahi Sarki Mukhtar, sun bankaɗo damin gwala gwalai
Jami’an hukumar yaki da zamba dayi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC sun dira gidan tsohon mashawarcin shugaban kasa Yar’adua akan lamarin tsaro, Abdullahi Sarki Mukhtar a ranar Laraba a wani samame da suka gudanar inda suka bankado wasu damin tarin zinari na miliyoyin nairori.
Gidan da jami’an suka kai samamen, gidan wani surukin Sarki Mukhtar ne, mai suna Akka Babba Danagundi, a nan ne jami’an EFCC suka gano wani katafaren asusu da baya jin wuta makare da gwala gwalalai a gidan dake lamba 375 a rukunin gidajen Gwangwazo cikin birnin Kano.
KU KARANTA: Tsohon babban sakataren ma’aikatar wutan lantarki ya yafe ma gwamnati motoci 47 da aka kwato a hannunsa
Duk a cikin wannan katafaren asusu, jami’an sun gano takardun shaidar mallakan gidaje guda hamsin (50) dake dauke da sunayen Abdullahi Sarki Mukhtar tare da Matarsa Binta Sarki Mukhtar
Jami’an sunce sun kai samamen ne bayan sun samu wani rahoton sirri dake nuna cewar da alamu an boye wasu makudan kudade samfurin dalaolin Amurka a gida. Sai dai jami’an sunyi gaba da Akka Babba Danagundi zuwa ofishinsu dake jihar Kano inda suka zazzage ma hukumar bayani
Wata majiya daga hukumar ce ta shaida ma jaridar Daily Trust a jiya, inda tace an kai samamen ne da misalin karfe 5 na yamma, inda tace an gano wasu muhimman takardu da dama.
Isar su babban ofishin EFCC keda wuya, sai aka bude wannan katafaren asusu, inda aka ciro sarkokin zinari da agoguna da takardun shaidan mallakar gidaje guda 50, wanda yawancin gidajen suna jihohin Kano, Abuja da Kaduna.
An samu agoguna guda 55, cikinsu har da na zinari, sai sarkokin zinari guda 37 da nauyinsu ya kai gram 1,907.9, da wasu sarkoki guda 15 na ado
Dag bisani an sallami dukkanin mutanen da aka kama, banda Danagundi wanda a yanzu haka yake taimaka ma hukumar da bayanai dangane da binciken da suke yi.
A cewar majiyarmu, hukumar ta samu bayanan sirri ne daga bakin wani bawan Allah daya fallasa Sarki Mukhtar.
Ga Hotunan nan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng