LABARI DA DIMI-DIMINSA: Majalisar dattijai ta tabbatar da Onnoghen a matsayin alkalin alkalan Najeriya
1 - tsawon mintuna
Majalisar dattijan Najeriya a ranar Laraba, 1 ga watan Maris ta tabbatar da babban mai shari'a Onnoghen a matsayi alkalin alkalan najeriya.
Majalisar dattijan Najeriya a karshe dai ta tabbatar da mai shari'a Walter Onnoghen a zaman tantancewarsa a matsayin alkalin alkalan Najeriya.
Majalisar dokoki ta gudanar da zaman tabbatar da mai shari'a Onnoghen yau Laraba, 1 ga watan Maris.
Majalisar ta bayyana farin cikin ta ga gabatar da Onnoghen, kuma ta jaddada cewa shugaban kasa ya gabatar da shi ne bayan dogowar tataunawa kuma bisa karfafa halinsa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng