Sabon farashin Dala a yau
Labaran da ke zuwa mana yanzu suna nuni ne da cewa Naira na ta kara daraja musamman ma a kasuwannin bayan fage in ake saida Dalar a kan N425.
A makon da ya gabata ne dai Farashin dala ya fadi sosai a karon farko a kasuwannin bayan fage na NAjeriya, kasa da mako guda bayan da babban bankin kasar CBN, ya bayyana matakin bunkasa samar da ita ga masu nema a bankuna.
Matsalar karancin dala a bankunan Najeriya wanda sakamakon rashin wadatar kudaden kasashen wajen a CBN, ya sa dalar ta yi ta tashin gwauron zabi, a kasuwannin bayan fage na kasar.
Wasu na ganin wannan ne dalilin da ya sa kayayyakiin masarufi da na amfanin yau da kullum suke kara hauhauwa, duba da cewa kasar ba ta faye fitar da kaya zuwa wasu kasashe ba.
Kazalika kudaden kasashen wajen da take samu ya ragu sakamakon rage sayen man fetur dinta da Amurka ta yi, da kuma janyewar masu zuba jari.
Wasu rahotannin ma sun ce a makon da ya gabata sai da aka sayar da duk dala daya a kan naira 516.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa
Da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng