Hadiza Gabon ta gana da Dan masanin Kano

Hadiza Gabon ta gana da Dan masanin Kano

-Fitacciyar jarumar finafinan Hausa Hadiza Gabon ta yi arba da tsohon jakadan Najeriya a majalisar dinkin duniya kuma Dan masanin Kano Yusuf Maitama Sule

-Dan masanin ya yi murna da gaisuwar da ta yi masa ya kuma yiwa jarumar addu’a da sa albarka wanda hakan ya burge da kuma ba mutane mamaki

Hadiza Gabon ta gana da Dan masanin Kano
Hadiza Gabon ta gana da Dan masanin Kano

Fitacciyar jarumar finafinan Hausa Hadiza Gabon ta gaisa da tsohon jakadan Najeriya a majalisar dinkin duniya kuma Dan masanin Kano Yusuf Maitama Sule.

A cikin wasu hotuna da jarumar ta sa a shafinta na Instagram, na nuna cewa Hadizan ta hadu da dattijon ne a cikin jirgin sama a wata tafiya zuwa wai wani wajen da ba ta bayyana ba.

Sai dai ta ce Dan masanin ya yi murna matuka da girmamashin da ta yi sannan kuma ta ce,

“…Yau na yi dace da ganawa da wannan mashahurin mutum, ya rike hannu na, ya yi min addu’a, sannan ya kuma shi min albarka …"

"Na amfana matuka daga kalaman da ke fitowa daga bakinsa mai albarka da daraja tamkar zinare”.

Hadiza Gabon ta gana da Dan masanin Kano
Hadiza Gabon tare da Daudu Galadanci Kuliya tsohon dan wasan kwaikwayo a talbijin

Wannan ba shi ne karo na farko da Jarumar finafinan ta durkusa tare da kai ziyara ga dattijai da kuma manya a al’umma ba, a kwanakin baya jarumar ta ziyarci Alhaji Daudu Galadanci wanda aka fi sani da Kuliya.

Kasancewarsa daya daga cikin tsaffin taurarin shirye-shiryen talbijin da suka yi fice a zamaninsu wanda kuma a yanzu ya ke fama da rashin lafiya ga kuma shekaru.

Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Hadiza Gabon ta yi fice a finafinan Hausa na Kannywood, ta kuma lashe kambin zama jarumar-jarumai a shekarar 2016.

Hadiza ta kuma yi fice a ayyukan sa kai da taimakon al’umma ta hanyar wata gidauniya da ta kafa mai suna Hadizatou Foundation.

Baya ga harshen Hausa da Ingilishi, jarumar ta na jin harshen Faransanci kasancewar an haife ta ne kasar Gabon.

Ga hoton bidiyon zanga-zangar goyon Buhari a Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng