Adadin hadarin motan da ya faru a Najeriya, yawan mutanen da suka mutu cikin shekaran 2013-2015 da kuma jihohi
Dubunnan mutane sun rasa rayukansu sanadiyar hadarin mota. Wannan abu na da ban takaici kuma kullun karuwa yakeyi.
![Yawan hadarin motan da ya faru a Najeriya cikin shekaran 2013-2015 da kuma jihohi Yawan hadarin motan da ya faru a Najeriya cikin shekaran 2013-2015 da kuma jihohi](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt1q6jaro032a.jpeg?v=1)
Yayinda mutane na ganin cewa laifin gwamnati ne na rashin gina hanyoyi na kwarai, wasu suna ganin cewa laifin direbobi maras bin dokokin tukin mota ne.
KU KARANTA: An aurar da zaurawa akalla 1500 a jihar Kano
Wata sabuwar rahoton da kungiyar Economic Confidential ta saki ya bayyana cewa cikin shekaru 3, anyi hadura 79,875 a titunan Najeriya. Wannan babban abin takaici ne. Ubangiji kadai ya san yawan mutanen da suka rasa rayukansu.
Kalli jihohin:
1. Jihar Ogun
Jihar Ogun ce jiha da hadain mota yafi aukuwa a wannan lokaci. Haduran mota 6442 ne suka faru.
2. Jihar Legas
A jihar Legas, hadura 6231 ne suka faru a wannan lokaci.
3. Jihar Kano
Jihar Kano ce ta zo na uku inda hadura 4869 suka auku cikin shekaru 3
4. Birnin tarayya Abuja
Birnin tarayya Abuja ce ta zo na 4 a jerin jihohin da hadura suka fi faruwa
5. Jihar Edo
A jihar Edo kuma hadura 3499 ne suka faru.
A shekaran 2013, rayukan 5,539 ne aka rasa a hadari, 4,430 a shekarar 2014, sannan 5042 a shekarar 2015.
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng