Faretin Sojoji da Hausa ya ja hankalin 'yan Najeria (Hoton Bidiyo)

Faretin Sojoji da Hausa ya ja hankalin 'yan Najeria (Hoton Bidiyo)

A wani lamari na banbarakwai wasu sojojin Najeriya sun yi fareti da Hausa wanda hakan ya ja hankalin 'yan Najeriya musamman a dandalin Sada zumunta da muharawa na Facebook

Faretin Sojoji da Hausa ya ja hankalin 'yan Najeria
Faretin Sojoji da Hausa ya ja hankalin 'yan Najeria

Ba kamar yadda aka sani ba, ko kuma aka saba ji da gani ba dangane da al'adar soji a duniya na yin rawar daji ko fareti da harshen Turanci.

Wasu sojoji a Najeriya sun fito da sabon salon yin wannan fareti da harshen Hausa kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito ta hanyar wani hoton bidiyo da ta sa a dandalin sada zumunta na Facebook.

A na jin cewa hoton faretin daga dukkannin alamu na wasu dakarun sojojin Najeriya ne da ke bakin daga yankin arewa maso gabashin kasar.

Sojojin kuma su na yin faretin ne a cikin nishadi da walwala a hali irin na taba-kidi-taba karatu, sai dai hakan ya janyo ka-ce-na-ce a dandalin sada zumunta da Muhawara a inda kowa ke bayyana ra'ayinsa.

Yayin da wasu ke ganin hakan ya yi dai dai, kuma kamata a mayar da shi batu na kasa, wasu kuma na ganin wannnan wani mataki ne na Hausantar da kuma musuluntar da Najeriya, wasu kuma na ganin hoton bidiyo ya fito da cututtukan kabilanci, da bangaranci, da kuma banbancin addini da 'yan Najeriya ke fama da su.

Sai dai yayin 'yan Najeriya ke tada jijiyar wuya, su kuwa sojojin sun yi ta mahaukaci ne da ya fada a rijiya, watau kanku a ke ji, domin su dai nishadi kawai su ke yi daga dariya da sowar 'yan uwansu da ke kallo.

Ga hoton bidiyon

Asali: Legit.ng

Online view pixel