Shiriya daga Allah: Mabiya addinin kirista su 15 sun musulunta a jihar Kwara

Shiriya daga Allah: Mabiya addinin kirista su 15 sun musulunta a jihar Kwara

Jaridar Nairalanda ta ruwaito labarin wasu mutane su 15 da suka musulunta a jihar Kwara wadanda suka hada da Fasto da mabiyansa goma sha hudu.

Shiriya daga Allah: Mabiya addinin kirista su 15 sun musulunta a jihar Kwara
Shiriya daga Allah: Mabiya addinin kirista su 15 sun musulunta a jihar Kwara

Wani ma’abocin karanta jaridar mai suna Dahwah007 ne ya labarta ma Nairalanda labarin, wanda yace lamarin ya auku ne yayin wani taron wa’azi da kungiyar da’awa ta ‘Academy for Islamic propagation’ (ACADIP) ta shirya.

KU KARANTA:'Ɗaliban firamari a jihar Katsina sunyi ma shugaba Buhari addu’ar samun sauƙi

Dahwah007 ya bayyana cewar jimillan mabiya addinin kirista 15 ne suka musulunta a ranar, inda ya kara da cewa kungiyar ta musuluntar da kiristoci 316 a watannin shidda da suka gabata.

Shiriya daga Allah: Mabiya addinin kirista su 15 sun musulunta a jihar Kwara
Shiriya daga Allah: Mabiya addinin kirista su 15 sun musulunta a jihar Kwara

Dahwah yace: “a wannan taron wa’azin da muka shirya wanda ya fara tun a ranar juma’a 24 ga watan Feburairu da misalin karfe 10 na safe a garin Offa dake jihar Kwara, kungiyar ACADIP ta musuluntar da kiristoci 15.

“hakan kuwa ya faru ne bayan wata lakca da shehin malami Alhaji Yusuf Adepoju ya bayar tare da mujadala da aka yi tsakaninsa da wani Fasto tare da mabiyansa, sanadiyyar haka ne Faston da mabiyan anasa su 14 suka karbi musulunci. Cibiyar ta musuluntar ta mutane 316 a tsakankanin watanni 6 da suka gabata a jihohi da daman a kasar nan.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel