Kai yaro ne kuma babban makaryaci – Amaechi ga Nyesom Wike

Kai yaro ne kuma babban makaryaci – Amaechi ga Nyesom Wike

- Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya siffanta gwamna Nyesom Wike a matsayin makaryaci kuma yaro

- Amaechi yace kashe-kashe a jihar Ribas ta yawaita ne bayan Wike ya dau ragamar mulki

Kai yaro ne kuma babban makaryaci – Amaechi ga Nyesom Wike
Kai yaro ne kuma babban makaryaci – Amaechi ga Nyesom Wike

Tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya tuhumci gwamnan jihar Nyesom Wike da karya kuma yaro.

Jaridar Daily Post ta bada rahoton cewa Amaechi, a wata hira da gabatar da Abuja, ya tuhumci Wike da kokarin boye ayyukan da yayi lokacin yana gwamnan jihar ta hanyar canza sunan wasu ayyukan.

Yace: “Bai kamata gwamna yayi karya ba,amma idan aka zabi dan yaro a matsayin gwamna, zaku ga juye-juye iri-iri.

“Akwai wani Magana da ake cewa idan ka baiwa karamin yaro abinda ba zai iya dauka ba, zai ta tangadi ne. asibitocin da na gina har yanzu ana amfani da shi; yayi kokarin canza sunan daa daga cikin wanda na gina a cikin jami’ar kimiya da fasaha jihar Ribas.

“Makaryacine. Likitoci 200 na samu da na zama gwamna, na daki Karin 400. Kana karya ma yayi cewa ban biya albashin watanni 6. Duk wanda ke da hujja ya zo yzce ban biya albashin wata Afrilun kafin na bar ofis ba.”

“Makarantun firamaren da na gina har gobe babu mai kyan su a Najeriya. Dukka sunaa dakunan komfuta amma wannan gwamnati ta kulle shi.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng