Yadda wani masallaci ya zama mai fuskar Coci a Afrika ta Kudu

Yadda wani masallaci ya zama mai fuskar Coci a Afrika ta Kudu

- Wani ginin coci matsohon tarihi a Afirka ta Kudu ya zama masallaci kuma kuros din da aka yi ado da ita a hasumayar gaban cocin har yanzu tana nan.

- Ginin an yi shi ne tun shekarar 1903, shekaru 114 wanda daga bisani aka sayar wa da wani dan kasuwa a shekarun 1990s.

- An kirawo wasu masu zane-zane da ado irin na musulunci daga kasar Maroko su mayar da cikin cocin zama masallaci.

Yadda wani masallaci ya zama mai fuskar Coci a Afrika ta Kudu
Masallaci a ciki, Coci a waje a birnin Durban ta Afrika ta kudu

Musulmai a Durban ta Afirka ta Kudu su ka karbi wani tsohon coci sun kuma mayar da ita masallacin Juma'a.

An mayar da wani Coci mai tsohon tarihi a Africa ta Kudu masallaci, sai dai hukuma ta hana sauyawa wajen ginin kamanninsa na asali zuwa masallaci.

Haka kuma masallacin mai kama da majami'a har yanzu ya na tare kuros a can saman hasumayar sa wacce aka gina kimanin shekaru 114 da suka wuce.

Tsohuwar majami'ar da aka kira da Aliwal Congregational Church, an fara gina ta ne a 1903 inda daga bisani aka sayar wa da wani dankasuwa a shekarun 1990s.

Duk da cewa a yanzu an mayar da cocin masallaci, ginin zai ci gaba da karbar baki wadanda ba musulmai ba da su ke sha'awar ganin yadda ake yin sallah.

Ba kuma zai zama wajen sallah ba kawai, a sabon masallacin ma'aikata na kokarin samar da wajen bajen bajekolin hotuna da lakcoci da za a rika gabatarwa lokaci-lokaci a cikin ginin.

Musulman Durban sun dauko masu taswira kwaliyar gine-gine daga Maroko domin su mayar da ginin yanayin ginin musulmai daga ciki.

Yanzu dai masu taswirar sun shafe kimanin wata biyu su na kawata masallacin da alamomin musulunci.

Masallacin ya ci gaba da zama da kuros saboda duk abin da ke wajen Cocin na karkashin kariyar doka.

A karshe ya zama gurin bauta da ya hada manyan addinan guda biyu. Kirisatanci da kuma muslunci.

Don ganin wasu misalan majami'u da su ka rikide zuwa masallatai, kalli hoton bidiyon da ke kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng