Shahararrun ýan ƙwallon Duniya musulmai masu zuwa aikin Hajji akai akai
Kusan za’a iya cewa babu wasan motsa jiki a duniya da aka fi kallo kamar kwallon kafa, wato wasan tamola sakamakon da wuya kaje wani gari ko kauye baka tarar da al’ummar wurin suna buga ta ba.
Yan kwallon sune wadanda aka fi sanya ma idanu a yayin buga kwallon fiye da kowa, don haka muka kawo muku jerin sunyen wasu shahararrun yan wasan kwallon kafa Musulmai dake zuwa aikin hajji akai akai don bautan Allah.
1. Paul Pogba
Idan ka biye ta sunan dan wasan, sai ka zata ba musulmi bane, sai dai Paul Pogba cikakken musulmi ne, kuma har ya samu damar sauke farali ta hanyar zuwa hajji a rayuwarsa, ban da Umara da ya sha zuwa.
2. Emmanuel Adebayor
An haifi Adebayor, tsohon dan wasan Arsenal a shekarar 1984, ranar 26 ga watan Feburairu, kuma asalinsa mabiyin addinin Kirista ne tare da iyayensa da danginsa.
Amma a kwanan nan ne Adebayor ya canza addini, ya musulunta, kuma ya bada hujjar musuluntar tasa. Bayan karbar musuluncin nasa ne, sai Adebayor ya kai ziyara dakin Allah domin aikin Hajji a kasar Saudi Arabia.
KU KARANTA: ‘Jihar Kogi ta zama matattarar yan Boko Haram’ – Inji gwamna Yahaya Bello
3. Mesut Ozil
Masana kwallon kafa sun tabbatar Mesut Ozil na cikin gagga gaggan yan kwallon duniya, wanda ko a kasar sat a haihuwa Jamus, an dade ba’a samu kamar sa ba. Sai shima Ozil musulmi ne, kuma yana gudanar da aikin Hajji a duk shekara.
4. Abou Diaby
Haka zalika tsohon dan wasan Arsenal Abou Diaby wanda yanzu ya koma buga wasa a kungiyar Marseille shima musulmi ne, kuma yayi aikin Hajji ba sau daya ba, ba sau biyu ba.
5. Nicolas Anelka
Tsohon dan wasan Arsenal da Chelsea, Nicolas Anelka musulmin kirki ne sosai, kuma ya jajje kasa mai tsarki don gudanar da aikin Hajji.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng