Manyan yan siyasa 5 da ake sa ran zasu gaji Buhari a 2019
Biyo bayan cakudewar harkokin siyasa musamman ma a matakin gwamnatin tarayya tun bayan da rashin lafiyar shugaba Buhari taki ci taki cinyewa, yan Najeriya sun fitar da sunayen mutane 5 da ake tunanin zasu iya maye gurbin shugaba Buharin a zabe mai zuwa na 2019.
1. Sanata Rabi'u Kwankwaso
Masu bibiyar al'amurran kasar nan dai ka iya fahimtar cewa farin jinin Kwankwaso ya fara karade dukkanin daukacin arewacin Najeriya. Mutane da yawa suna ganin daga Buhari to kam sai Kwankwaso indai wajen farin jini ne. Wannan zai yi matukar tasiri idan har aka kada gangar siyasar.
2. Sanata Bola Tinubu
Mutane da dama musamman daga kudancin kasar nan sunyi amannar cewa kwarewar siyasa ta wannan dan tahalikin kadai ta isa ya gaji Shugaba Buhari idan hara yaso hakan don kuwa kusan dukkan yan siyasar kudancin kasar nan cikin aljihun sa suke.
Wani karin damar da zai samu shine idan har arewa ta fitar da mutane da dama wajen takarar wanda hakan zai iya kawo rarrabuwar kawuna daga bangaren.
3. Farfesa Osinbajo
Yanzu haka dai babu dan siyasar da tauraruwar sa ke haskawa kamar shi musamman ma idan akayi duba da yadda yake nuna kwarewa wajen salon mulkin sa tun bayan da Shugaba Buhari ya bashi ragamar mulkin kasar kafin ya tafi hutu da jinya a kasar Ingila.
Mutane da dama kuma na ganin kyakkyawar alakar sa da shugaba Buhari ma wata dama ce gare shi wajen ganin ya gaji uban gidan nasa.
4. Atiku Abubakar
Wannan gawurtaccen dan siyasa ne da yake da magoya baya a dukkan sako da lungun kasar nan. Atiku har ila yau wani mutum ne wanda bai taba boye sha'awar sa ta zama shugaban kasa ba wata rana don tuni har ya fara nuna alamun cewa zai fayi takara a zabe mai zuwa.
5. Sanata Bukola Saraki
To wannan dai yafi kama da maganar nan ta hausawa da suke cewa zakaran da Allah ya nufa da cara don kuwa matsan da yake rike da shi a yanzu ma haka jam'iyyar sa bata amince masa ba ya zama. Yanzu haka kuma shine na 3 a matakin girman mulki a Najeriya.
Mutane da dama suna ganin zai yi anfani da wannan damar tashi sosai musamman ma ganin yadda yake da goyon bayan manyan yan siyasa da bangaren jam'iyyar adawa ta PDP.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa
Da kuma tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng