Jerin sunayen mutanen da hukumar EFCC ke nema ruwa a jallo
Hukumar yaki da zamba, cin hanci da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ya bayyana jadawalin sunayen wasu mutane da hukumar ke nemansu ruwa a jallo sakamakon zarge zarge da dama dake wuyansu.
EFCC ta sanya sunayen mutanen ne a shafinta na yanar gizo, inda tace mutanen sun arce daga kasar tun bayan fara nemansu. Wasu daga cikinsu sun hada da:
1- Ekpemupolo A.K.A Tompolo
Aiki: shugaba a kungiyar tsagerun Neja Delta, MEND
Tuhuma: aikata miyagun laifuka, da tsere ma shari’a
Kudin sata: Naira miliyan 34
2-Bawa Thomas Momodu
Aiki: Ma’aikacin bankin Sterling, reshen garin Fatakwal
Tuhuma: Bindiga da kudi, hada takardun bogi da satar kudi
Kudin sata: Naira miliyan 27
KU KARANTA: Ahir! ‘Ba’a shiga tsakanin Buhari da Osinbajo, danjuma ne da dan jummai
3-Emeka Charles Ekekwe
Aiki: Tsohon ma’aikacin bankin Fidelity
Tuhuma: Satar kudin kamfani
Kudin sata: Naira miliyan 146
4-J. Ogbonna Obike Phillip
Tuhuma: Safarar makudan kudade dayace babban banki ta tura mai akan kuskure
Kudin sata: Naira miliyan 45
5- Abdulrasheed Maina
Aiki: Tsohon shugaban hukumar fansho
Tuhuma: cin kudin yan fansho, karkatar da kudaden yan fansho
Kudin sata: sama da naira biliyan 2
6-Mariano Albino
Tuhuma: Zamba cikin aminci, bindiga da kudade
Kudin sata: Naira miliyan 989, 288, 400
7- Desmond Osawaru
Tuhuma: Zamba
Kudin sata: dala 200, 000
8- Ibrahim Saminu Turaki
Aiki: Tsohon gwamnan jihar Jigawa
Tuhuma: wadaka da kudaden al’umma, da satar kudaden al’umma
Kudin sata: sama da naira biliyan 30
9- Badmus Luqman Adedeji
Aiki: shugaban kamfanin motoci na KYC dake Kaduna
Tuhuma: satar kadarorin bankin First Bank
Kudin sata: Naira miliyan 40
10- Nsikak Anthony Usoro
Aiki: dan asalin karamar hukumar Mkat dake jihar Akwa Ibom
Tuhuma: kuskuren aikawa da kudaden jiha
Kudin sata: Naira miliyan 107
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng