Abubuwa 12 game da marigayi Sheikh Ja'afar wadanda tarihi ba zai manta da su ba

Abubuwa 12 game da marigayi Sheikh Ja'afar wadanda tarihi ba zai manta da su ba

Tarihin ba zai manta da fitaccen shaihun Malami a mai wa'azin addinin muslunci Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ba wanda aka yiwa kisan gilla a Kano a cikin shekarar 2017

Abubuwa 12 game da marigayi Sheikh Ja'afar wadanda tarihi ba zai manta da su ba
Abubuwa 12 game da marigayi Sheikh Ja'afar wadanda tarihi ba zai manta da su ba

Ga wasu abubuwa guda 12 game da malamin wadanda za a dade ba a manta da su ba a tarihi abubuwa na 4 da na 5 za su fi ba ka mamaki game da marigayin

1. Haihuwarsa

An haifi marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam a garin Daura, a shekara ta 1962 (ko da ya ke wani lokacin ya kan ce 1964),

2. Karatun Allo

Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, wurin Mijin yayarsa Malam Haruna, daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen Malam Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda kuma shi ne musabbabin zuwansa Kano a shekara ta 1971 (ko 1972), ya kuma zauna a makarantar Malam Abdullahi a unguwar Fagge a Kano.

3.Haddar Kur'ani

Marigayin ya fara haddar Alkur'ani mai girma yana karami, ya kuma kammala a shekarar 1978.

4. Karatun Boko na yaki da jahilci

Kasancewarsa mai sha'awar ilimi, Sahaihun malamin ya shiga makarantu biyu a lokaci guda; makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra Markaz a cibiyar yada Al ' Adun Misra, (Egyptian Cultural Centre) da ke Kano, da kuma makarantar manya ta yaki da jahilci a makarantar Firamare ta Masallaci a shekarar 1980, ya kuma kammala a 1983.

5. Karatun Sakandare

Wannan ya ba marigayin damar shiga makarantar GATC Gwale a shekara ta 1984, wacce ya kammala a shekara ta 1988.

6. Jami'a

A shekara ta 1989, sheikh Ja'afar ya samu gurbin karatu a Jami'ar musulunci ta Madinah a kasar Saudiyya, a inda ya karanta Ilimin Tafsiri wacce kuma ya kammala a shekarar 1993.

Sannan ya kuma samu damar Kammala karatunsa na digiri na biyu digiri da digirgir (Masters) a Jami’ar Kasa-da-Kasa ta Afrika da ke Khartoum a kasar Sudan.

Kafin rasuwarsa, ya samu gurbin karatunsa na digiri na uku, wato Dakta (Phd), a Jami' ar Usman dan Fodiyo a Sokoto.

7. Wadanda suka karantar da shi

Daga cikin malamansa na ilimi, akwai malaminsa na farko, mutumin kasar Masar, Sheikh Abdul-Aziz Ali al-Mustafa, da kuma Malam Nuhu a unguwar Dandago, wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu Littattafai na hadisi a gurinsa, da kuma Malam Muhammad Shehu, mutumin Lokoja, wanda Malam ya karanci Nahawu da sarfu, da Balaga da kuma adab a wajensa.

Akwai kuma Jibrin Abubakar Sheikh Limamin Masallacin Juma ' at BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano. Daga cikin malamansa na jami'a kuma, akwai Sheikh Abdurrafi ' u da Dr.. Khalid Assabt.

8. Wasu daga cikin dalibansa

Wasu daga cikin daliban malam sun hada da Malam Rabi ' u umar R/Lemo da Malam Sani Abdullahi Alhamidi dorayi da Abdullah Usman G / rich da Malam Usman Sani Haruna da Ibrahim Abdullahi Sani da Malam Yunus Ali Muhammad da Dr.. Salisu Shehu da Malam ShehuHamisu Kura da Muhammad Madabo.

8. littafan da ya koyar da su

Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar da su, sun hada da tafsirin Alkur'ani maigirma, kitabuttauhiid, Umdatul Ahkaam, Arba'in Hadiith, Kashfusshubuhaat, Bulugul Maraam, Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz, Siffatus salaatun nabiiy.

9. Rubuce-rubucensa

Kafin rasuwarsa, malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin wata cibiya mai suna Cibiyar adana bayyanai ta Sheikh Ja'afar.

10. Rasuwarsa

Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya rasu a ranar Juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 (13/04/2007) sakamakon wani hari da wadansu 'yan bindiga 'yan ta'adda suka kai masa, a daidai lokacin da ya ke jagorantar sallar asuba a Masallacin Juma ' a na Dorayi.

11. Jana'izarsa

Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan suka Halarci Jana ' Izarsa, kuma an binne shi ne a makabartar Dorayi.

12. Iyali

Ya rasu ya bar mata 2, da 'yaya 6 yayin da aka haifa masa ta 7 kwanaki 58 a daidai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa.

Ga wani hoton biyon jin ra'ayin jama'a kan 'yan arewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng