Yadda manzon Allah ﷺ ya kwadaita mana tausayin talaka
Rayuwan manzon Allah tamkar rayuwar talaka bawan Allah ne.
Ummuna Aisha ta ruwaito cewa “ Iyalan manzon Allah basu taba koshi na kwanaki 3 a jere ba har ya rasu .” (Al-Bukhari)
Manzon Allah na kula da talaka d tausayi da kuma rahama, ya kasance yana basu suk abinda suke bukata duk da cewa shi ma ba su yake da shi ba. Kana kuma yanan kwadaitar da sahabbansa su dinga nuna tausayi ga talakawa.
Yace : "Ya kai dan Adam! Ya fi maka alkhairi ya kashe kudin ka, amma idn ka rike su, sharri zasu zame maka….."
Tausayin manzon Allah (S.A.W)
Birnin Madina ta kasance matalauciyar gari, akwai lokacin da manzon Allah ya fadawa Abu Dharr cewa “Abu Dharr, duk lokacin da ka daura sanwa, ka kara ruwa sannan ga gayyaci makwabcinka (Muslim)
Manzon Allah ya kwadaitar da Abu Dharr hakan ne duk da cewa Abu dharr ma talaka ne.
Kana kuma yana fadawa matan sahabbai su dinga kyautatawa makwabtansu: Kada waninku yayi tunanin kofaton tinkiya yayi kadan ga makwabcinsa ( Muslim).
https://twitter.com/naijcomhausa
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
Asali: Legit.ng