Zamu hana 'talaka' auren mace fiye da daya - Sarkin Kano
- Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce majalisarsa tana shirye-shiryen samar da wata doka da za ta hana mazan da basu da karfi auren mata fiye da daya a jihar
- Sarki Sunusi ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taro a Abuja na tunawa da marigayi Ambasada Isa Wali, wanda ya mutu shekaru 50 da suka wuce
Ya ce yawan aure-aure da mutane ke yi alhalin basu da karfin rike iyali kamar yadda shari'ar Musulunci ta tanada, yana matukar yin mummunan tasiri wajen tarbiyyar yara da basu ilimin da ya dace.
Hakan a cewarsa saboda yadda talauci ke dabaibaye iyayensu ga rashin basu kulawar da ta kamata yasa mafiya yawa daga cikin irin wadannan yara na karewa ne a mastayin 'yan daba ko 'yan ta'adda.
Sarkin ya ce zai tabbatar da cewa dokar ta bi dukkanin hanyoyin da suka dace domin gwamnatin jihar ta Kano ta tabbatar da ita.
Mai martaba ya yi nuni da cewa abin takaici ne yadda za a ga mutum yana fama da cin yau da na gobe, amma zai auri mace fiye da daya, ya kuma haifi 'ya'ya masu yawan da ba zai iya ciyar da su ba, ko tufatar da su, ko samar musu da isasshen muhalli ba, ballantana ya basu irin tarbiyyar da al'umma za ta yi alfahari da su.
Ya ce mutane suna fassara damar da Musulunci ya bayar na auren mace fiye da daya ba daidai ba.
Kuma a yawancin lokuta ba tare da sun cika sharuddan da addini ya tanada ba na kara auren.
Dama tun kusan shekara daya da ta gabata ne, Sarkin ya kafa kwamitin malaman don yin nazari tare da tsara yadda dokar za kasance kafin gabatar da ita a gaban majalisar dokokin jihar.
Sarkin Kano dai ya ce dokar za ta zama wani bangare na tunawa da marigayi Ambasada Wali, wanda ya kasance daya daga cikin mutanen Arewacin Najeriya na farko da ya yi aiki tukuru don tabbatar da daidaito tsakanin jinsi.
Kano ita ce jihar da ta fi kowacce jiha yawan al'umma a Najeriya, kuma a can ne aka fi samun yawan mace-macen aure.
Sai dai kuma wasu na ganin auren mata fiye da daya da mazan marasa karfi ke yi a jihar yana taimakawa wajen rage yawan mata da zawarawa da ke zaune ba miji.
Inda ko a shekarar 2013 ma gwamnatin jihar ta aurar da zawarawa 1111, a karkashin tsarin auren da hukumar Hizba ta jihar ke shiryawa.
Asali: Legit.ng