Namiji ya samu juna biyu bayan anyi masa dashen mahaifa (Hoto/bidiyo)

Namiji ya samu juna biyu bayan anyi masa dashen mahaifa (Hoto/bidiyo)

Kamar yadda hausawa ke cewa, Bambarakwai, namiji da suna Hajara, toh haka ne ta faru yayi da wani fitaccen mawaki dan kasar Afirka ta kudu Somizi Mhlongo ya samu juna biyu, wanda a yanzu haka yake dauke da shi.

Namiji ya samu juna biyu bayan anyi masa dashen mahaifa (Hoto/bidiyo)
Namiji ya samu juna biyu bayan anyi masa dashen mahaifa (Hoto/bidiyo)

Dayake dai an samu rahoton daukan cikin nasa ne ta majiyoyin karkashin kasa, amma dai yanzu ana sauraren jawabi daga Mhlongo da kansa.

Majiyoyin sun tabbatar mana da cewar Mhlongo ya samu juna biyun ne bayan anyi masa aiki na musamman a kasar Brazil inda aka yi masa dashen mahaifa, inda aka sanya masa dan karamin jariri a cikin mahaifar, inji majiyar. Majiyar ta kara da cewa a watan Janairu ne aka yi ma Mhlongo dashen.

KU KARANTA: Allah Sarki: Ta kwankwaɗa ma yaronta kalanzir, ca take ruwa ne

Namiji ya samu juna biyu bayan anyi masa dashen mahaifa (Hoto/bidiyo)
Namiji ya samu juna biyu bayan anyi masa dashen mahaifa (Hoto/bidiyo)

Wani aminin Mhlongo yace, Mholongon na cikin farain ciki matuka bayan samun juna biyun, “yana jin dadi da zarar yaji jaririn na harbi a cikinsa.” Inji aminin nasa.

Idan rahotannin suka tabbata, ya kasance kenan Mhlongo ne mutum na farko a nahiyar Afirka daya fara samun juna biyu. Sai dai aikin dashen mahaifan bada matukar hatsari inji aminin Mhlongo.

“Sai mutum ya cika wasu sharudda masu tsauri sosai har na tsawon shekaru biyu, daga bisani idan aka samu wanda jininku yazo daya sai, kuma zata baka mahaifa, sai ayi maka dashe.” Inji shi.

A shekarar 2008 ne dai aka fara samun rahoton samun nasarar dasa ma namiji mahaifa, yayin da aka dasa ma wani mutum mai suna Thomas Beatie wanda ya fara zama namiji mai juna biyu a duniya.

Namiji ya samu juna biyu bayan anyi masa dashen mahaifa (Hoto/bidiyo)
Namiji ya samu juna biyu bayan anyi masa dashen mahaifa (Hoto/bidiyo)

Yadda ake yin wannan aiki kuwa, shine sai an samu maniyyin namiji, sai a sanya a cikin mahaifar wata mace, daga nan kuma sai a dasa ma mutum, sai dai zuwa yanzu ba’a san wanene uban jaririn da aka dasa ma Mhlongo ba, amma wasu na kusa da Mhlongo sun ganin wata kila Lundi Tymara ne.

Sai dai jama’a da dama sun caccaki lamirin Mhlongo dayaje yana kashe makudan kudade akan aikj banza dana wofi.

Ga bidiyon namiji mai juna biyu, Mhlongo

Mu a nan sai dai muce Allah ya tsayar akansu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel