Allah Sarki: Ta kwankwaɗa ma yaronta kalanzir, ca take ruwa ne
Wani karamin yaro dan watanni 18 mai suna Israel Buhari ya mutu har lahira bayan mahaifiyarsa ta dura masa kalanzir, tsammaninta ruwan sha ne, a garin Bini.
Rahotanni sun bayyana cewar Buhari ya nemi mahaifiyarsa wanda take siyar da kalanzir da ta bashi ruwa ya sha, amma tsautsayi ya sanya mahaifiyar tasa dauko kalanzir da aka dura a cikin roban ruwa ta kwankwada ma yaron.
Wannan tsautsayi ya auku ne da misalin karfe 10 na safe a layin Iguma dake garin Bini ranat Talata 14 ga watan Feburairu.
KU KARANTA: Gwamnatin tarayya zata miƙa Zakzaky hannun gwamnatin jihar Kaduna
Shi dai yaro Buhari shine da namiji guda daya tal da matar ta haifa cikin yayanta guda hudu, kuma rahotanni sun nuna cewar Buhari ya furzar da kalanzir din bayan ya sha, daga nan ne uwar yaron ta fahimci abinda ya faru, kafin kace kule, idon Buhari yayi fari fat, kuma yana ta ihu.
Daga nan sai makwabta suka kawo mata agaji, suka dura ma yaron manja, daga bisani aka garzaya da shi asibiti, inda yace ga garinku nan bayan wasu yan awanni.
Yayin da take bayani, uwar yaron, Uwargida Ata Buhari yar asalin jihar Kogi tace daya daga cikin yaranta ne ya dura kalanzir a cikin roban ruwa, wanda suke siyarwa, sai dai tace itama tana da ruwa dauke cikin kwatankwacin wannan roban a shagon, don haka yayin da yaron ya nemi ya bashi ruwa, sai kawai ta dauko roba daya ta bashi, ashe na kalanzir ne.
Shima mahaifin yaron, Buhari Hassan dan asalin jihar Kogi yace kiransa aka yi ya garzaya asibiti da gaggawa, inda daga isa sai gawar dansa aka ba shi, daga nan sai ya roki gwamnati da masu hannu da shuni dasu taimaka mai da iyalansa sakamakon talauci daya mu katutu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng