Karanta sirrin Dangote 9 game da kasuwanci

Karanta sirrin Dangote 9 game da kasuwanci

- Kasancewar sa mamallakin kamfanin Dangote da ke samar da kayayyakin masarufi iri-iri a Najeriya da wasu kasashen Afirka ba wasa ba ne.

-An kiyasta yawan dukiyar Dangote ta kai Dalar Amurka biliyan 12.5 yayin da mujallar Forbes ta bayyana shi a matsayin wanda ya fi kowa kudi a Afirka kuma na 67 a jerin masu kudin duniya.

Karanta sirrin Dangote 9 game da kasuwanci
Karanta sirrin Dangote 9 game da kasuwanci
Asali: Facebook

Duba ka ga wadansu hanyoyi da ya nuna su ne maksudin nasararsa ga wadanda su ke son zama kamarsa:

1. Tsayawa guri daya

Babban attajirin ya shawarci 'yan Najeria su dinga tsayawa guri daya a duk abin da su ke yi. Tsallen badake daga waccan sana'a zuwa wannan ba tare da cin nasara ba, ba abu ne mai kyau ba.

2. Sauraron jama'a

Daya daga cikin mabudan nasarar Dangote da ya fada da bakinsa ga masu son cin nasara a rayuwa, shi ne sauraro. Dole ne ka saurari jama'a kuma ka tsaya ka koya a wajensu, hakan zai taimaka ma ka samu ilimi daga bangarori daban-daban.

3. Tunani don gobe

Wannan zai taimaka wa mutane da dama su yi adabo da gasa a harkokin kasuwanci. Wannan hanya mai muhimmanci ta na iya nufin tsara al'amura don gaba.

Kawai za ka iya cin nasara ne yayin da ka fara hangen abin da zai zo gaba sannan ka shirya masa. Akwai matakai da ya kamata ka bi wajen hangen nesa.

Karanta sirrin Dangote 9 game da kasuwanci
Karanta sirrin Dangote 9 game da kasuwanci

4. Hangen Nesa

Kokarin samun nasara ba ta lokaci ne, in har ba ka da hangen nesa. Me za ka yi? A wace irin harka za ka samu nasara?

5. Mai da hankali

Dangote bai ta ba yin wata harka da ba shi da ilimi a kanta ba. Aliko Dangote ya bayyana wannan a daya daga cikin hanyoyin samun nasararsa ma fi amfani. Ka gujewa duk wani abu da zai dauke ma hankali daga harkokinka.

6. Ka samu sahihan bayanai

Tsunduma cikin harka ba tare da saninta ba, ba abu ne da zai haifar da da mai ido ba. Dangote ya ce, bai taba shiga wata harka ba, ba tare da ya samu sahihan bayanai game da ita ba. Ka da ka yanke gurguwar shawara saboda rashin sani.

7. Zuzzurfan tunani

Yin zuzzurafan tunani ba zai zama matsala ba tun da ba zai sa ka asara ba. A cewar Dangote kwakwalwarka daya ce, kuma ya rage na ka ka fadada tunani, ko ka kuntata shi. Ba wanda ya ke biyan kudi don ya yi zuzzurfan tunani. Bai kamata ka takaice kanka da dan abin da ka sani ba.

Karanta sirrin Dangote 9 game da kasuwanci
Karanta sirrin Dangote 9 game da kasuwanci

8. Sunanka Jari ne

Yayin da ka ke kokarin cin nasara a rayuwa, ya kamata ka lura da abubuwan da ka ke yi. Kar ka zubar da mutuncinka yayin da ka ke kokarin shahara.

Ya kamata duk abin da ka ke kokarin ginawa ya zama ba bu almundahana a ciki. Sunanka da na kamfaninka babban jari ne da ya kamata a bawa kariya.

9. Ka samu ingantattun tsare-tsare

Tunanin wata harka, ba daya ya ke da tsare-tsaren da za su kawo sakamakonta ba. Dole ne ka samar da tsare-tsaren da za su taimaka wajen kafuwar harkar. Yayin da kake cikin ta, yana da muhimmanci ka yi harkar da ka fahimta.

Ra'ayin jama'a kan lafiyar Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng