Tarihi : Sarkin Musulumai wanda ya kare mutuncin Kiristoci

Tarihi : Sarkin Musulumai wanda ya kare mutuncin Kiristoci

Ameer Abdul Qadir Al-Jazairi, daya daga cikin manyan malaman musulunci. Ya kasance babban malamin addini, sarki, dan kasuwa kuma mabiyi koyarwan manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi).

Tarihi : Sarkin Musulumai wanda ya kare mutuncin Kiristoci
Tarihi : Sarkin Musulumai wanda ya kare mutuncin Kiristoci

Amma lokacin da ya koma kasar Turkiyya bayan yayi zaman kurkuku a kasar Faransa, duk masu gadin gidan yarin Faransa sun musulunta sanadiyar shi.

Daga baya sai Napoleon ya gane cewa ashe an zalunci wannan mutumi, sai ya kawoa birnin Faris kuma yayi masa kyauta, duk da cewa sun kwace masa garinsa.

Ya koma kasar Turkiyya kafin ya koma birnin Dimashka a karnin 1860 inda ya tarar an cin zarafin Kiristoci. Sai ya mike tare da yan kasan Aljeriya suka kare Kiristocin.

Yace: “ Kuma saba umurnin manzon Allah. Mutanen nan basuyi muku komai ba kuma ya kamata a karesu.”

Yanzu, daya daga cikin mutanen da ya kare jakadan Faransa ne, duk da cewa sun kwace masa garinsa bayan ya yake su tsawon shekaru 20. Ya kre shi duk da cewan ya ganeshi.

Kawai sai wannan abu ya birge jakadan Faransan har yayi rubutu akansa a jaridar kasan Faransa. A lokacin ne ya shahara.

Thackeray ya rubuta wata kasida akanshi. An ambacesa a majalisar turai, kana kuma Amurka ta san da shi. Akwai garuruwa 2 a Amurka da sanya wa sunansa.

Shugaba Grant yayi mamakin halin kirkkinsa har ya aika masa da doki da bindigogi 2 a mastayin kyauta. Amma Ameer Abdul Qadir Al-Jazairi ya fadawa mabiyansa cewa kare mutuncin kiristoci karamin jihadi ne…. Lokacin da muke yaki a Aljeriya da kiristoci, kare kasarmu mukeyi.

Lokacin da wani ya tambayeshi me yasa addinin kirista tafi musulunci yaduwa yanzu, yace dalili shine musulmai sun bar addinin su. Kuma Allah na daurasu akanmu ne saboda mun tozarta addinin Allah kuma yanzu muna tozartar da kanmu.

Kalli bidiyon tarihinsa:

Asali: Legit.ng

Online view pixel