Addinin Musulunci bai yarda da nuna bambamcin launin fata ba
- A kowane lokaci mu kan tsinkaye munanan labarai a kafafen sadarwa, labarai irin na yakuna, miyagun ayyuka, bala’o’i da sauransu. Wannan ya kan sanya mutane cikin firgici
- Duk da firgicin da hakan zai sanya mu ciki, mutum mai hankali ya kamata ya tambayi kansa wai ina duniyar mu ta yau zata damu ne da irin fitintinun nan?
Daya daga cikin abubuwan dake zama silan haddasa rikita rikitan nan shine wariyar launin fata, shine ya biyo mu tun daga zamanin baya, har yanzu, inda wasu ke ganin har abada wasu na kasan su kawai saboda bambamcin launin fata.
Shin menene wariyar launin fata?
Wariyar launin fata itace tunani ko zato da wani mutum zai sanya a ransa na cewa yafi karfin wani mutum na daban ta duba da yanayin halittarsa, kuma za’a iya famintar lamarin ta ganin cewar farar fata tafi bakar fata, don haka kowa bai kamata a hada su ba a komai.
Sai dai musulunci yayi tir da wariyar launin fata, kamar yadda Allah yace a Sura:49:13
“Ya ku mutane, mun halicce ku daga abu daya, namiji da mace, kuma muka rarrabaku kabilu da kasashe, don ku fahimci junanku. Amma ku sani wanda yafi matsayi a wajen Allah shine mafi tsoron Allah.”
Wannan ayar tana magana ga dukkanin mutane ne, ba musulmai kawai ba, don haka musuluci ya koya mana yan’uwantaka da juna, haka zalika musulunci ya haramta nuna bambamci ta kowane hali.
Musulunci bai yarda wani ya nuna bambamcin a dangane da kabila, launin fata, yare ko arziki ba, shima Annabi Muhammad ya tabbatar da haka a wa’azin bankwana. Inda yace:
“dukkanin mutane sun zo daga Adam da Hauwa’u ne, balarabe ba shi da wani fifiko fiye da wanda ba shi ba, haka zalika shima wanda ba balarabe ba, bai fi wanda ba shi ba; farar fata bata fi bakar fata ba, kamar yadda itama bakar fata bata da fifiko fiye da farar fata, sai dai ta ayyuka kyawawa da tsoron Allah.”
KU KARANTA: An samu ɓullar wata annoba a makarantar sakandari a Zamfara
Wani mutum ya kawo ma Annabi ziyara a madinah, sai yaga wasu mutane suna tattauna batutuwan daya shafi addini, cikinsu akwai Salmanul Farisi, Suhaib dan kasar Roma da kuma Bilal dan yankin Afirka. Mutumin ya kada baki yace:
“Idan kabilun Madina Aws da Khazraj sun bi Annabi Muhammad, ai larabawane kamar sa. Amma wadannan me suke yi a nan?”
Nan fa sai ran Annabi y abaci bayan an kai masa kara, sai ya wuce masallaci ya sanya aka tara mutane don yayi musu jawabi: “ya ku mutane, ku sani Allah daya ne. asalinku ma daya ne, addininku daya ne, larabcin da kuke ji da shi ba wani abu bane face yare, kuma ba wai daga iyayenku kuka same sa ba duk mai yin larabci, balarabe ne.”
Wariyar launin fata na da muni
Ya kamata musulmai mu gane cewar nuna bambaci kowane iri baya cikin koyar addini, don haka ya dace mu tarbiyantar da yaran mu akan haka, mu nuna musu haramcin nuna wariyar launin fata.
Wariyar launin fata na rarraba kawunan musulmai, kuma hakan ke halatta ma wasu mutane cin zarafin wasu ba tare da jin komai ba. Allah ya halicce mu Uwa daya Uba daya, ma’ana dukkanin mu abu daya ne, kuma ta hanya daya aka haife mu.
Dole ne mu fahimci cewar Allah daya ne, kuma Shi ya halicce mu bangarori daba daban, kuma wannan alama ne da Ubangiji ya sanya tsakanin mu, kamar yadda Ya fada a Qur’ani:
{kuma daga cikin alamomin Sa akwai halittar sammai da kassai, da kuma bambamcin harsunanku da launin fatan ku. Don haka wannan wa’azi ne ga ma’abota ilimi.} (31:22)
Idan an lura ba’a kwatanta kalmar kabila da wata kalma ba a cikin wannan ayar nan ko a wani aya. Sai dai musulunci ya iyakance iya bambamce bambamcen da ake nunawa. Ba’a yarda ayi amfani da wannan hujjar wajen cin mutuncin juna ba akan kabilanci, kasasa, mulkin mallaka da wariyar launin fata.
Dayawa daga cikin matsolilin da muke fuskanta a yau halayen mu ne suka janyo mana sakamakon rikicin akida, inda mutane ke yakar juna ba tare da lura da cewar abubuwan da suka hada su sun fi abubuwan da suka raba su yawa ba. Ya kamata a gyara.
Mu dinga tuna cewar Allah ya kawo bambamce bambamcen ne don mu mutane su samu cigaba da kwanciyar hankali. Lallai mu sani dan adam baa bin wulakantawa bane, dole a girmama shi.
Muslunci ya koyar damu ta samun tsoron Allah, matukar tsoronsa ne kawai wani ko wasu zasu iya samun daukaka. Don haka ne ma ya dace mu dinga tunawa da wasu abubuwa guda 2: Yi ma kai fada, da kuma tadabburi akan halayen mu.
Ya kamata mu dinga duba halayen mu, tare da lura da yadda muke mu’amala da mutane tare da gayra kurakurenmu da zarar mun farga, duk mutumin dake da tsoron Allah zaka same shi yana gudun miyagun ayyuka, kuma yana rungumar kyawawa, da wannan ne kadai mutum zai samu daukaka fiye da wani.
Sai dai kash! Shi kuwa tsoron Allah ba’a iya gane shi a fuska ko a auna, Allah kadai ya sani, don haka ya dace mu daina yanke ma mutum hukunci kawai daga ganinsa.
Wariyar launin fata a Yammacin duniya
An tabbatar da cewar wariyar launin fata mummunan abu ne, amma duk da haka yana gudana a kullum, na yi sa’a matuka yadda a matsayin na musulmi na taso a kasar da ba ta musulmi ba, na tabbatar sa’ace kawai na samu.
Dayake dai ba’a nuna min wariya sosai ba, amma fa na sha fama a yayin da ake cin mutuncin mu da sauran yaran unguwa. Na tuna wani dan babban aji ya taba tambayata wai ina Ghandi yake, a zatonsa dan Inidiya ne ni, nan da nan nace masa ban sani ba.
Amma daga bisani sai shi dan babban ajin Tutankhamen ya yaba min, ya bani hakuri, daga nan kuma muka fara abota, daga nan bai kara tsokana nab a, kuma bai sake tsokanan wani ko wata ba.
Akwai hanyoyi da dama da ake bi wajen nuna wariyar launin fata, kamar su zambo, ba’a, zagin kabila ko yare, cin mutunci ko ma dukan mutum saboda launin fatarsa. Wata kila sai da na girma na fahimci Nelson Mandela tare da fahimtar halin da yan kasar Afirka ta kudu suke ciki, daga nan ne na fara karatu, ina fahimta. Daga nan na gane lallai ya kamata a zauna lafiya a duniya.
Ko yanzu da nake rubuta wannan, ana yawan samun tashin tashina, musamman rikicin yansandan kasar Amurka da matasan bakaken fata, ko kuma rikicin falasdinawa da isra’ilawa, na kasa gane alakar hakan da yada tsarin dimukradiyya, don haka wannan yaci karo da koyarwar musulunci.
Na gano cewar idan wani abu ya kasance abin dariya, toh na yarda kowa yayi dariya, amma ba abin dariya bane idan hakanz ai sosa ran wani. Na san na taba karantawa wani zance da Charlie Chaplin yayi, inda yace “muna da yawan tunani, amma muna da karancin damuwa. Don haka muna bukatar halayya mai kyau, da tausayawa, da tausasawa.”
Amma kafin mutum ta samu mukamin nan, sai ya dinga damuwa da halin da wani ke ciki ba tare da nuna bambamcin kabila, launi ko addini ba.
Annabi Muhammad yace: “Duk wanda ke da kwayar zarra na girman kai ba zai shiga aljanna ba, wani mutum yayi tambaya game da girman kai, idan ya sanya kyayawan tufafi, sabbin takalma, girman kai ne? sai Annabi yace Allah kyakkayawa ne, yana son kyawu. Sai ya kara bayani girman kai shine kin karbar gaskiya saboda jiji da kai tare da raina mutane.” (Muslim)
Idan muna nuna damuwa da damuwar wasu, zamu iya kawar da wahal wahalun dake addabar mu, idan ba haka ba kuwa, zamu cigaba da fuskantar wahal wahalu daban daban, kuma hakan ba zai taba kawo zaman lafiya a duniya ba.
Ya kamata mu sani halittar dan adam ba karamin lamari bane, don haka lallai muyi amfani da damar mu yadda ya kamata kafin ta kufce mana, lallai mu sani don wani ya samu daukaka bai kamata ya wulakanata na kasa da shi ba.
Wannan shine koyarwar musulunci.
Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa/
Ko a https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng