Kungiyar Izala ta goyi bayan Shehu Sani yayi takarar Gwamna

Kungiyar Izala ta goyi bayan Shehu Sani yayi takarar Gwamna

Kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'ah Wa Ikamatus Sunnah reshen Jihar Kaduna ta yi Addu'ar Allah ya sanya Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya zama Gwamnan Jihar Kaduna a shekarar zabe ta 2019, sakamakon kwazo da Sanatan yake da shi wajen taimakon addini da taimakawa jama'a gaba daya.

Kungiyar Izala ta goyi bayan Shehu Sani yayi takarar Gwamna
Kungiyar Izala ta goyi bayan Shehu Sani yayi takarar Gwamna

Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na kasa na Kungiyar Sheik Yusuf Muhammad Sambo Rigachikum ya tabbatar da haka, lokacin da yake jawabin godiya ga Sanatan jim kadan bayan ya karbi takardar wani katafaren gida da dan Majalisar ya sayawa 'yan agaji na Kungiyar domin gudanar da aikace aikacensu a titin Lagos Street Unguwar Shanu Kaduna.

KU KARANTA: Ba haram bane shan giya indai bata sa maye ba inji wani malami

Sheikh Sambo Rigachikum ya cigaba da cewar samun mutum irin Sanata Shehu Sani a cikin Al'umma ba karamin cigaba bane, domin a fili yake Sanatan mutum ne Wanda a rayuwarshi ya damu da halin da Jama'ar da yake wakilta suke ciki, inda yayi fatan Allah ya shigewa Sanatan gaba akan ayyukan alheri daya sanya a gaba.

Lokacin da yake mayar da jawabi Sanata Shehu Sani ya bayyana cewar, babban abinda 'yan siyasa ke aiwatarwa lokacin gudanar da yakin neman zabe shine alkawura, amma abin takaici yawa yawan 'yan siyasa basa cika wadannan alkawura wadanda suka dauka, sabanin yadda ya wajabtawa kanshi baya samun natsuwa idan ya dauki alkawari sai ya cikashi, saboda haka sayawa 'yan agajin wannan gida da yayi wani bangare ne na cika alkawarin daya dauka lokacin yakin neman zabe.

Sanata Shehu Sani ya kuma bada kyautar wasu karin gidajen ga Kungiyar 'yan agaji Mata na Izala wadanda ake kira da sunan Nisa'us Sunnah a titin Ara dake Garin Kaduna, sannan ya bayar ga Kungiyar 'yan agaji na Fityanul Islamic mabiya darikar Tijjaniyah a garin Hayin Dan Mani dake Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng