‘Muslunci ne maganin dukkanin matsaloli’ inji masu karajin aiki da shari’ar musulunci a kasar Ingila (bidiyo)

‘Muslunci ne maganin dukkanin matsaloli’ inji masu karajin aiki da shari’ar musulunci a kasar Ingila (bidiyo)

Wani faifan bidiyo ya watsu a kafar sadar ta Youtube inda wasu musulman kasar Birtaniya ke kokawa kan matsalolin kasar, inda suka bukaci a tabbatar da shari’ar musulunci, hakan ne kadai hanyar warware duk wasu matsalolin da kasar ke fuskanta.

‘Muslunci ne maganin dukkanin matsaloli’ inji masu karajin aiki da shari’ar musulunci a kasar Ingila (bidiyo)

Sai dai wata musulma yar kasar Ingilan mai suna Tarek Fatah ta soki lamirin masu ikirarin tabbatar da shari’ar musulunci a kasar ta Birtaniya.

Fatah ta bayyana haka ne a shafinta na Twitter inda tace “musulman Birtaniya sun fusata, suna bukatar tabbatar da shari’ar musulunci a kasar Birtaniya. Wai shin mmeke damun mu?”

KU KARANTA: Ingantattun addu’o’i daga manzon Allah, Annabi Muhammadu (SAW)

A cewar wanda ya daura bidiyon Anuj Bhardwaj yace “Musulunci shine ingantacciyar hanyar da zata magance duk wani matsala. Kowa ya fara bin tsarin musulunci, kuma a tabbatar da shari’a muslunci a duk kasashen duniya. Allah daya ne, kuma babu abin bautawa da gaskiya sais hi kadai.”

Baya da matashin musulmin dake magana kan lallai sai an tabbatar da shari’ar musulunci a kasar Birtaniya a bidiyon, ana iya ganin wasu musulman suna daga takardu dake dauke da rubuce rubuce kamar su ‘musulunci ne maganin duk matsalolin mu.’

Sai dai har zuwa yanzu ba’a tabbatar da ranar da aka dauki bidiyon masu zanga zangar ba.

Ga bidiyon nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng