Abin al'ajabi: ƙaramar yarinya ýar shekara 5 ta haihu

Abin al'ajabi: ƙaramar yarinya ýar shekara 5 ta haihu

Kimanin shekaru tamanin (80) da suka gabata ne aka samu wata karamar yarinya a garin Andes na kasar Peru ta kafa tarihi, inda ta zamto uwa mafi kankancin shekaru bayan ta haihu yayin da take yar shekaru 5.

Abin al'ajabi: ƙaramar yarinya ýar shekara 5 ta haihu
Abin al'ajabi: ƙaramar yarinya ýar shekara 5 ta haihu

Ita dai wannan yarinya mai suna Lina Medina an gano tana dauke da juna biyu ne yayin da iyayenta suka lura cikinta ya fara girma, kuma tana yawan samun laulayi, hakan ya sanya iyayenta tunanin kodai gyambon ciki ne ke damun Lina Medina?

KU KARANTA: Allah ya kawar da mummuna hatsarin jirgin sama a jihar Legas

Amma daga bisani bayan kwararrun likitoci sun duba Lina, sai suka gano cewar yarinya Lina na dauke da ciki ne, wato juna biyu.

Abin al'ajabi: ƙaramar yarinya ýar shekara 5 ta haihu
Abin al'ajabi: ƙaramar yarinya ýar shekara 5 ta haihu

Haka dai Lina ta cigaba da dawainiya da cikin nata har zuwa lokacin data haihu, a shekarar 1938, inda ta haifi jariri namiji, amma sai da likitoci suka yi mata tiyata aka samu nasarar ciro yaron, nan da nan iyayen Lina sai murna, nan fa suka rada ma jaririn suna Gerardo.

Duk da cewa shekarun Lina kankani ne, amma likitoci sun tabbatar da cewar gabobinta sun nuna, don haka zata iya samun ciki da haifar da shi.

Sai dai, anyi zargin cewar mahaifin Lina Medina shine ya dibga mata ciki, amma dai an kasa tabbatar da wannan zargi, hakan ya sanya har yau ba’a gano wanene mahaifin Gerardo ba.

Wannan ya sanya Gerardo bai taba sanin cewar Lina itace mahaifiyarsa ba, har sai daya kai shekaru 10, sai dai a yanzu haka Gerardo ya rasu, bayan ya kwashe shekaru 40 a rayuwa, amma mahaifiyarsa Lina na nan da ranta, kuma tana da shekaru 85 a rayuwa yanzu haka.

Ga bidiyon labarin Lina Medina

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng