Maza 4 da budurwa 1 masu yankan kai sun shiga komar Ýansanda

Maza 4 da budurwa 1 masu yankan kai sun shiga komar Ýansanda

Wasu gungun yan yankan kai dasu hada da maza hudu mace daya sun shiga hannun yansanda a jihar Ebonyi yayin da aka kama su dauke da sabbin kawunan mutane guda hudu.

Maza 4 da budurwa 1 masu yankan kai sun shiga komar Ýansanda
Kawunan mutane agaban su

Da misalin karfe 10 na safiyar Laraba 8 ga watan Feburairu ne miyagun mutanen suka shiga hannun jami’a hukumar yansandan jihar Ebonyi daidai lokacin da aka tsare wata motar hayar da take dauke dasu yayin gudanar da binciken motoci a kan iyakar jihar Enugu da Ebonyi.

KU KARANTA: Wata mata ta roƙi kotu ta raba aurensu da mijinta saboda yawan duka

Jaridar Vanguard ta ruwaito wata majiyar gani da ido tana fadin cewar da alama daga jihar Enugu ne mutanen suka shigo jihar Ebonyi akan hanyarsu ta zuwa jihar Kros Riba.

Rahoton ya cigaba da fadin jami’an yansanda sun harbi mutanen a kafafunsu yayin da suka yi kokarin tserewa, bayan an kama su da sabbin kawunan mutane.

Daga bisani anyi awon gaba dasu zuwa wani wuri da ba’a tantance ba, sakamakon suma jami’an yansandan jihar Ebonyi basu bada karin bayani dangane da lamarin ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng