Yan matan jami'ar Legas sun yi tsokaci game da sabuwar dokar hana sa matsattsun kaya

Yan matan jami'ar Legas sun yi tsokaci game da sabuwar dokar hana sa matsattsun kaya

- Dalibai da dama sun tofa albarkacin bakinsu a matakin da jami'ar Lagos ta dauka na hana saka matsatsun kayan da ke nuna surar jiki

- A wata hira da majiyar mu ta yi da wasu daga cikin daliban, da dama daga cikinsu sun ce sun yi na'am da matakin inda suke cewa zai rage yawan alfasha da dabi'u marasa kyau tsakanin dalibai

Yan matan jami'ar Legas sun yi tsokaci game da sabuwar dokar hana sa matsattsun kaya
Yan matan jami'ar Legas sun yi tsokaci game da sabuwar dokar hana sa matsattsun kaya

Sai dai wasu daga cikin daliban sun ce bai kamata a tursasa musu a kan irin suturar da za su saka ba, inda akasarinsu ke cewa kamata ya yi a bi su ta lallami domin aiwatar da matakin.

A wani bangaren kuma, wasu daliban na ganin cewa tun da har suka kai matsayin jami'a ya kamata a kyale su su zabi irin kayan da ransu ya ke so a lokutan da suke so su saka.

Sai dai hukumar makarantar, wadda ta ce ta dade da daukar wannan matakin, ta yi hakan ne domin ganin cewa a mafi yawan lokuta yanayin suturar da dalibai ke sawa na taka rawa wajen gurbata tarbiyya da aikata ayyukan da basu dace ba.

A wasu lokutan ma hakan kan jawo a yi wa mata fyade ko makamantan su.

Amma hukumar makarantar ta ce zuwa yanzu an fara samun raguwar irin wadannan munanan dabi'u sakamakon bin doka da daliban ke yi, inda yanzu suka fi yin shigar mutunci fiye da shiga mai nuna al'aura.

Hukumar makarantar dai ta hana sa kayan da suke matse jiki ga maza da mata, da kuma sa kayan ado na kawa kamar zinare da dogayen 'yan kunne masu jan hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel