Abubuwa 6 na kamanci tsakanin Buhari da 'Yar'aduwa
A lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da tsawon hutunsa, tsoron lafiyar shugaban ya shiga zukatan 'yan Najeriya.
Wannan ya sa ‘yan Najeriya tuna da shekaru 2010, a lokacin da tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar'adua ya yi wata rashin lafiya wanda ta jefa al’umma kasar cikin duhun kai.
Menene kamance tsakanin Shugaba Buhari da kuma marigayi Yar’aduwa?
1. An haife su a jihar Katsina
An haifi shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Disamba 17, 1942 a garin Daura jihar Katsina ga mahaifinsa Adamu da Zulaihat Buhari.
Marigayi Umaru Musa Yar'Adua kuma an haife shi ne Katsina a watan Agusta 16, 1951 ga wani tsohon ministan birnin Lagos na jumhuriyar farko.
2. Sun samu goyan bayan shugaba Obasanjo
Tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo, ya fito fili ya bayyana goyon bayansa ga Muhammadu Buhari a lokacin neman zabe wanda ya kazance dan takara jam’iyyar APC, ya yin da Yar'aduwa shi ya gabatar da marigayi Umar Yar'Adua ga matsayi na shugaban kasa.
3. Sun kasance da rashin lafiya a ofishin
Marigayi tsohon shugaban kasa Yar'Adua ya yi rashin lafiya a lokacin da ya ke mulki a inda aka kai shi kasar Saudi Arabia saboda nema magani kafin Allah ya masa cikawa a watan Mayu a shekara 2010.
Shugaba Muhammadu Buhari kuma yana fama da rashin lafiya a inda ya nema wata tsahon hutu zuwa Ingila da kuma neman magani.
4. Sun sanya mataimakin shugabannin su a addashin Shugaban kasa
A watan Fabrairu 9, 2010, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda yake mataimakin Yar’aduwa ya zama addashin shugaban kasa domin Shugaba Yar'Adua ya tafi zuwa Saudi Arabia domin yin jinya.
Shugaba Muhammadu Buhari shima ya sanya mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo a matsayin addashin shugaban kasa a karo na uku cikin shekaru biyu bayan da ya fara wata hutu a wata Janairu 19, 2017.
KU KARANTA KUMA: Mutane 6 sun hallaka a wata arangama a jihar Filato
5. Sun sanya kasar a cikin wata rudani
Rashin sani takamamman lafiyar tsohon shugaban kasa marigayi Yar'Adua ya sa ‘yan Najeriya rashin tabbas da abin da ke faruwa . A halin yanzu kuma haka yake faruwa da shugaba Muhammadu Buhari.
6. Sun fifita zuwa asibitin kasashen waje
Shugabannin biyu sun fifita zuwa kasashen waje domin lura da kiwon lafiyar su.
Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa
http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng