Bincike: ko kasan yawan tarin arzikin Aliko Dangote? (KARANTA)

Bincike: ko kasan yawan tarin arzikin Aliko Dangote? (KARANTA)

Duniyar ta maliki yaumiddini cike take da hamshakan attajirai, sai dai kamar yadda hausawa ke cewa, so so ne, amma son kai yafi, kuma ai dama da arziki a gidan wasu, gwara a gidanka. Wannan ya sanya mu kawo muku cikakken bayani kan tsagwaran arzikin attajirin Najeriyan nan Alhaji Aliko Dangote.

Bincike: ko kasan yawan tarin arzikin Aliko Dangote? (KARANTA)

Mutumin daya fi kowa arziki a Afirka:

Wannan mutumi ba wani bane illa kasaitaccen attajirin nan mai suna Aliko Dangote dan mutan kanawa wanda ya shahara a fannin kasuwanci irin na sarrafa siminti, tare da harkar suga, fulawa, gishiri sai man fetur da dangoginsu. Kuma a yanzu haka ya fara gina matatan man fetur a Najeriya, wanda ba kamarsa a kasar.

Da fari dai Aliko Dangote jikane ga hamshakin attajirin nan na dauri wato Alhaji Sanusu Dantata wanda ya shahara a jihar Kano, kuma yayi tasiri wajen tarbiyantar da jikan nasa tun yana dan kankani. Aliko Dangote ya taba cewa “zan yi tuna sadda nake makarantar firamari, na kan je in sayo kwalayen alawa, sai in je in siyar don kawai in samu kudi, tun a wancan lokacin nake da sha’awar kasuwanci.”

Aliko Dangote ya fara ne da kamfanin ‘Dangote Group’ inda suke hada suga da fulawa, gishiri, yadudduka, gidaje, siminti da har mai da isakar gas. Kusan suke dauke da kaso mafi tsoka na cinikayyar kayayyakin abinci a Najeriya. Sai dai kamfanin nasu ya samu alfarma irin na siyasa sosai.

Tsagwaran arzikin Aliko Dangote:

A shekarar 2017 an lissafa tarin arzikin Dangote ya kai dalan amurka biliyan 12 da miliyan 500 ($12.5 billion)

A lissafin na shahararriyar jaridar kasuwancin nan Forbes, tace Dangote ne na daya a Najeriya, kuma 68 a Duniya.

Motocin Aliko Dangote:

An san attajirai da son hawa motocin alfarma don kece raini, shima dai Dangote ba’a bar shi a baya ba. Don wasu daga cikin motocinsa sun hada da:

• Mercedeses

• Maybach’s

• Buggati’s

• Bentleys

Bincike: ko kasan yawan tarin arzikin Aliko Dangote? (KARANTA)

Katafaren gidan Aliko Dangote na Alfarma:

A yan kwanakin da suka gabata ne Aliko Dangote ya baiwa wata gidan talabijin damar shiga gidansa don dauko hoton gidansa dake babban birnin tarayya Abuja. Dangote ya kwashe kusan shekaru 12 yana zaune a gidan tare da iyalinsa.

Bincike: ko kasan yawan tarin arzikin Aliko Dangote? (KARANTA)

Amma a yanzu haka gidan na kasuwa, ida ake son siyar da shi saboda ya siya wani sabon gida a birnin Landan, amma fa gidan nasa na Abuja ya amsa sunan gida saboda tsabagen kayan ado da kawa da suka cika gidan.

Bincike: ko kasan yawan tarin arzikin Aliko Dangote? (KARANTA)

Shima Dangoten yace “talabijin wani basira da zai baka daman samun kayatarwa daga mutanen da ba zaka iya kawo su gidanka ba. Ina yawan kallon talabijin, musamman tashoshin kasuwanci, kamar Bloomberg, ina jiran ranar da zamu samu babban gidan talabijin a nahiyar Afirka.”

KU KARANTA: Hotuna 7 na yadda attajiran larabawa ke almubazzaranci da kudi

Jirgin ruwan yawo na Aliko Dangote:

A shekarar 2013 ne Dangote ya siya wani katafaren jirgin ruwa na yawon shakatawa mai cike da kayayyakin kawa akan farashi mai tsada sosai.

Bincike: ko kasan yawan tarin arzikin Aliko Dangote? (KARANTA)

Jirgin saman Aliko Dangote:

Haka zalika a yan kwanakin nan Dangote ya siya wani kasaitaccen jirgin sama don sawwaka a kansa zirga zirga tsakanin kasashen duniya, kuma ya siya wannan jirgi ne a ranar bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa, akan dala miliyan 45.

Bincike: ko kasan yawan tarin arzikin Aliko Dangote? (KARANTA)

Sai dai wani abin alfahari da Dangote shine yana taimakawa wajen daukan ma’aikata a kasar sa, inda a yanzu yake da sama da ma’aikata 110, 000 a Najeriya. Dangote yace “bari in fada maka wani abu, babu abinda zai taimaki kasar Najeriya kamar su yan Najeriyan su dawo da kudaden su kasar. Idan yau zaka bani dala biliyan 5, dukkaninsu zan zuba su a Najeriya. Dole ne mu taimaki kawunan mu.”

Bincike: ko kasan yawan tarin arzikin Aliko Dangote? (KARANTA)

Bugu da kari Aliko Dangote yana da halin kirki sosai, inda a kwanaki ya bada kyautan dalan amirka biliyan 2 da miliyan 200 don kyautata rayuwanr yan Najeriya da inganta Ilimi.

Ga bidiyon gidan Dangote nan:

Asali: Legit.ng

Online view pixel