An kara kudin shiga jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja

An kara kudin shiga jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja

A yau Litinin ne, hukumar kula da jiragen kasa (NRC) ta bayar da sanarwar yin karin kudin shiga jirgin kasa daga Kaduna zuwa Babban birnin Tarayya Abuja da kashi 25 wanda kuma tuni ya fara aiki.

An kara kudin shiga jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja
An kara kudin shiga jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja

A bisa sabon tsarin farashi, daga yanzu fasinjojin da ke amfani da taragar marasa karfi, za su rika biyan Naira 1,050 a maimakon Naira 600 sai kuma masu amfani da taragar Alfarma za su rika biyan Naira 1,500 a maimakon Naira 900.

A wani labarin kuma, Gwamnatin Najeriya ta amince da a karo sababbin taragon jirgen kasa domin jigilan matafiya daga Kaduna zuwa Abuja.

Ministan Sufuri, Hadi Sirika ne ya sanar da hakan wa manema labarai a fadar gwamnati dake Abuja.

Ministan yace gwamnati tayi hakanne ganin yadda matafiya zasu karu musamman daga Kaduna zuwa Abuja nan da wata mai zuwa a dalilin gyaran filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja da za’a fara.

Filin jirgin saman Kaduna ne za’a yi amfani dashi domin hada-hadan jiragen sama wanda hakan yasa za’a samu Karin yawan mutanen da zasu dinga bin hanyar daga Kaduna zuwa Abuja da kuma Abuja zuwa Kaduna.

Kwanakin baya gwamnati ta bada kwangilan gyaran hanyar Kaduna zuwa Abuja duk saboda hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng