Hukumar kula da tashoshi jiragen ruwa, NPA, ta jinjina ma Kwastam

Hukumar kula da tashoshi jiragen ruwa, NPA, ta jinjina ma Kwastam

Shugaban hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa na kasa (NPA) Hajiya Hadiza Bala Usman ta yaba ma shugaban hukumar kwastam ta kasa kanal Hamid Ali mai ritaya da jami’an hukumar sakamakon kama bindigu guda 661 da suka yi wadanda aka yi kokarin shigo dasu Najeriya.

Hukumar kula da tashoshi jiragen ruwa,NPA, ta jinjina ma Kwastam

Hajiya Hadiza ta bayyana ma manema labaru haka ne ta bakin Kaakakin hukumar NPA, Michael Ajayi a ranar Lahadi 5 ga watan Feburairu.

A cewarta, hukumar NPA ta gamsu da yadda hukumar kwastam ta kama sundukin dake dauke da makaman bayan ya fita daga tashar jirgin ruwan Legas.

KU KARANTA: Yadda wani hafsan soja ya keta haddin wata kurtun soja

Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito Ajayi yana fadin “wannan wata alama ce dake nuna hukumar kwastam ta sanya matakai masu tsauri na ganin ta tabbatar ba’a shigo da makamai kasar nan ba. Da ba dan an kama makaman nan ba, tabbas da Allah kadai ya san iya asarar rayukan da zasu janyo a kasa.”

Daga nan sai Hajiya Hadiza ta shawarci hukumar data fadada binciken ta game yadda aka shigo da makaman. Sa’annan ta bukaci dukkanin hukumomin tsaro dake aiki a tashar tashin jiragen ruwa dasu zage damtse wajen ganin ba’a sake samun wannan matsala ba.

Daga karshe ta shawarci jama’a dasu dinga baiwa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar basu labarin duk wani abin da suka gani da basu gamsu da shi ba don magnce wannan matsalar a gaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel