Ba fulani bane ke haddasa rikicin kudancin Kaduna - Janar Buratai

Ba fulani bane ke haddasa rikicin kudancin Kaduna - Janar Buratai

- Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya Janar Yusuf Tukur Buratai da gwamnan jihar Kaduna sun dora tubalin gina barikin soja a Kafanchan cikin kudancin jihar ta Kaduna

- Yayinda suke dora tubalin ginin barikin sojan a garin Kafanchan Janar Buratai ya kara nanata maganar da ake cewa wasu bakin haure ne suka kawo rikici a kudancin jihar Kaduna

Ba fulani bane ke haddasa rikicin kudancin Kaduna - Janar Buratai
Ba fulani bane ke haddasa rikicin kudancin Kaduna - Janar Buratai

Janar Buratai yace wajibi ne al'ummar jihar Kaduna su dinga tunawa sun dade tare suna zama lafiya saboda haka su gujewa duk wani bakon hauren da zai zo ya raba kawunansu.

Yace sun lura ya kamata a gina barikin soja a yankin domin a samu tsaro da zaman lafiya. Yace kamar yadda sarkin Kagoro yayi bayani Fulanin dake haddasa rikici a yankin daga kasashen dake makwaftaka da Najeriya suka fito.

A nashi jawabin gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai yace kafin ma a kammala ginin gwamnatinsa zata duba ta ga gidajen da zata iya ba sojoji domin a kawosu a jibgesu a Kafanchan cikin gaggawa da zummar dakile duk wani yunkurin tashin hankali.

Yace kammala ginin barikin zai dauki shekaru kuma shekarun ne basu da su. Idan so samu ne ko gobe ma a kawo sojojin domin su kare al'ummar yankin.

Dangane da kokarin da gwamnatin jihar keyi na kawo karshen tashin tashina a jihar Gwamna El-Rufai yace binciken da suka yi ya nuna an yi tashe-tashen hankali sau goma sha daya a jihar kuma idan Allah ya yadda ba zasu bari na sha biyu ya auku ba.

Gwamna El- Rufai ya sha alwashin hukumta duk wadanda aka samu suna da hannu a rikicin jihar kuma ko wanene, har da cewa ko dan cikinsa ne aka samu da laifi za'a hukumtashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel