Gwamnatin Kano zata dauki malamai 2,000 aiki

Gwamnatin Kano zata dauki malamai 2,000 aiki

Nan bada dadewa bane gwamnatin jihar Kano zata kara yawan malaman makarantun gwamnati a jihar Kano ta hanyar daukan sabbin malamai guda dubu biyu da zasu yi aiki a makarantun firamari da na karamar sakandari.

Gwamnatin Kano zata dauki malamai 2,000 aiki

Yayin dayake jawabi a taron horaswa na hukumar ilimi a matakin farko ta jihar wato SUBEB, Mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Hafiz Abubakar yace gwamnatinsu tana baiwa bangaren ilimi muhimmanci sosai, inda yace “a shekarar 2016 kadai, mun kashe sama da naira biliyan 30 a albashin ma’aikata.”

KU KARANTA: Yadda wani hafsan soja ya keta haddin wata kurtun soja

Mataimakin gwamnan yace malaman da za’a dauka aiki su dubu biyu sun samu shaidar kammala karatun NCE ne a karkashin daukan nauyin gwamnatin jihar, kuma akwai wasu malaman su 25,000 da suke yin karatun NCE da na gaba da digiri a fannin ilimi, duk a aljihun gwamnatin jihar.

Farfesa Hafiza cikin abubuwan da za’ayi don bikin satin malamai, akwai ganawa tsakanin gwamna Ganduje da malamai 1000, shuwagabanannin kungiyoyin malamai da iyaye su 44, da sauran masu ruwa da tsaki a harkar Ilimi.

“Manufar shirya wannan ganawa da gwamna shine don tattauna batutuwan da suka shafi bangaren Ilimi tare da nemo hanyar warware su. tun bayan hawar mu karagar mulki zuwa yanzu, mun kashe kudade sama da naira miliyan 811 a wajen manyan ayyuka a makarantu.” Inji shi

Hafiz ya jaddada manufar gwamnati na yin tafiya tare da al’umma musamman a fannin ilimi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng