Yadda wani hafsan soja ya keta haddin wata kurtun soja

Yadda wani hafsan soja ya keta haddin wata kurtun soja

Wata kurtun soja daga rundunar mayakan sojan sama mai suna Igbobie Uzezi zargi wani hafsan soja shima dake rundunar mayakan sojan sama mai suna B.S Vibelko mai mukamin Flight lieutenant da laifin yi mata fyade bayan ya bata kayan maye ta sha a shekarar 2011.

Yadda wani hafsan soja ya keta haddin wata kurtun soja
Igbobie Uzezi

Uzezi ta gurfanar da sojan da ya aikata mata wannan aika aikan, tare da hukumar mayakan son sama, babban hafsan sojan sama da ministan shari’a saboda korarta da aka yi daga sojin ba tare da ka’ida ba.

KU KARANTA: Yan majalisa zasu hana bare riƙe shugabanci kwastam

Lauya Malachy Ugwummadu na kwamitin kare hakkin bil adama ne ya shigar da kara mai lamba FHC/L/CS/10/17 a madadin Uzezi gaban babban kotun tarayya dake jihar Legas.

Kotu tace “yin fyade ga Uzezi babban cin mutuncinta ne da tauye mata hakkinta a matsayinta na mace tare da cin zarafin matantakanta.”

Uzezi na tuhumar Vibelko da laifin aikata mata fyade a ranar 17 ga watan Mayun 2011, inda tayi ikirarin hart a kamu da cutukan da ake samu ta hanyar saduwa sakamakon afkawar da sojan yayi mata.

Cikin karar da Uzezi ta shigar, ta ce “bayan faruwar lamarin, sai aka daure ne a sansanin sojojin sama dake Victoria Islan jihar Legas, cikin wani halin kuntatawa da horo mai tsanani har na tsawon kwanaki 14 daga 9 ga watan Mayu zuwa 23 na shekarar 2013.

Kuma babban hafsan sojin sama, kwamandan sojin sama da shi kansa sojan sa yayi min fyaden ne suka bada umarnin daure ni ba tare da gurfanar da ni gaban kotu ba ko kuma su fada min laifina.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel