Zaman lafiya yafi zama ɗan Sarki: Za’a sulhunta rikicin kudancin Kaduna

Zaman lafiya yafi zama ɗan Sarki: Za’a sulhunta rikicin kudancin Kaduna

Kabilu mazauna yankin kudancin Kaduna tare da hadin gwiwar kungiyar kiristocin kasar nan, CAN, reshen jihar Kaduna sun yanke shawarar tattaunawar sulhu da yan Fulani mazauna yankin don kawo karshen rikice rikice da suka addabi yankin.

Zaman lafiya yafi zama ɗan Sarki: Za’a sulhunta rikicin kudancin Kaduna
Za’a sulhunta rikicin kudancin Kaduna

Hakan na daya daga cikin matakan da aka yanke sakamakon zaman tattaunawa da aka yi tsakanin wakilan addinai da kabilu sama da 60 wanda cibiyar samar da zaman lafiya na kasa (GPFN) ta shirya akan warware rikce rikice daya gudana a garin Kachia ranar Laraba.

Dayake karin bayani a bayan kammala taron, kaakakin cibiyar GPFN Richard Pius Garba yace sakataren kingiyar CAN Rabaren Sunday Ibrahim ya nanata bukatarsu na ganin an hau teburin tattaunawa da Fulani makiyaya don shawo kan rikicin kudancin Kaduna.

KU KARNTA: Sojoji sun kama manyan kwamandojin Boko Haram guda 5

Shima wakilin kungiyar World Alliance for Development Mista Jonah Yahaya ya jaddada bukatar mutane da su zauna lafiya tare nuna jin kai ga juna don hakan ne zai janyo hankalin masu zuba jari tare da kawo cigaba ga al’ummarsu.

Zaman lafiya yafi zama ɗan Sarki: Za’a sulhunta rikicin kudancin Kaduna
Cibiyar GPFN yayin gudanar da taron

Hakazalika wakilin kungiyar KAICIID reshen Najeriya Mista Joseph Atang ya shawarci al’ummar yankin dasu mayar da wukakensu cikin kube, don samun kwanciyar hankali, tare da bayyanar da masu tada kayar baya a tsakaninsu.

Shima malamin musulunci Sheikh Halliru Maraya ya nanata cewar babu wata cigaba da zai samu al’umma ba tare da sun rungumi zaman lafiya ba, sa’annan ya shawarci jama’a dasu dinga neman sulhu a matsayin hanyar magance matsalolinsu.

Tun da fari, shugaba cibiyar GPFN John Oko yayi bayanin dalilin wannan taro, inda yace sun shirya shi ne don samar da hanyar magance matsalolin tsaro, inda yace da tun a baya ma sun tattauna da yan Fulani makiyaya wajen kawo karshen rikita rikitan.

Muna nan a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel