Sojoji sun kama manyan kwamandojin Boko Haram guda 5

Sojoji sun kama manyan kwamandojin Boko Haram guda 5

A kokarinta na kakkabe matsalar ta’addanci a kasar nan, musamman a yankin Arewa mso gabas, rundunar mayakan sojan kasa ta bayyana nasarar kama wasu gagga gaggan kwamandojin kungiyar Boko Haram su biyar.

Sojoji sun kama manyan kwamandojin Boko Haram guda 5
Manjo janar Lucky Irabor

Kwamandan yaki da Boko Haram, Manjo janar Lucky Irabor ne ya shaida ma manema labarai hakan a ranar Alhamis 2 ga watan Janairu a garin Maiduguri.

Irabor yace sun samu nasarar kama yan ta’addan ne da taimakon kungiyar tsaro na yan sa kai wato ‘Civilian JTF’

KU KARANTA: Miji, mata da ýaýansu 3 sun rasu a haɗarin mota

Manjo janar Irabor ya bayyana sunayen wadanda aka kama kamar haka: Alhaji Madu mai shekaru 56, Abur Goni- Bukar, Ibrahim Ali, Ayuba Duse da Haruna Bukar

“Mun kama su ne bayan gudanar da samame daban daban a yankuna daban na Arewa maso gabas, amma muna gudanar da bincike kafin daukan mataki akan su,” inji shi.

Babban kwamandan yace a ranar 27 ga watan Janairu ma dakarun soji sun kama wasu yan Boko haram mutum uku dauke da kayan abinci da suka hada da fulawa, gyada da gero wanda zasu kai kauyen Jeram, inda yace an samu kudi N594,000 a tare dasu.

“Haka zalika a ranar 28 ga watan Janairu, sojojin mu sun kama kama yan Boko Haram su biyar a cikin wata babbar mota cike da sinadarin ‘gypsum’ da suke amfani da shi wajen hada bom.” Inji Irabor

Daga karshe yace suna nan suna gudanar da bincike akan su suma.

Muna nan a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng