Wani mutum ya yi wa shekau korarin shigar wutar Jahannama
Kane marigayi Farfesa Aliyu Usman Mani ta Jami'ar Maiduguri ya lahananci shugaban 'yan boko Haram Abubakar Shekau a wata budeden wasika.
Malam Usman Abbas, kane marigayi Farfesa Aliyu Usman Mani, wanda aka kashe a lokacin wani harin kunar bakin wake a Jami'ar Maiduguri (UNIMAID), ya ce Abubakar Shekau matace ne a raye wanda makomarsa wutar Jahannama.
Usman ya bayyana wannan a cikin wani budeden wasika ga Abubakar Shekau, shugaban Boko Haram a wata bangare. Jaridar News gency ta Najeriya (NAN) ta rahoto wannan labari ranar Alhamis a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Na saurari sautin sakon ka inda ka ce ka dauki alhakin harin kunar bakin wake da ya kashe dan'uwana Farfesa Aliyu Usman Mani da wayansu a lokacin sallah asuba a masallacin ma’aikatar Jami'ar Maiduguri babban birnin jihar borno a ranar Litinin 16 ga watan Janairu, 2017.
KU KARANTA KUMA: Rashin tabbatar da alkalin-alkalai dan Cross Rivers ya jawo kace-nace
Jawabi na a wannan wasika zuwa gare ka shine wuta jahannama ne makoma duk wanda ke hallaka rayuwar al’umma.
Sabanin da'awar ka a cikin mafi yawan bidiyo da kuma sautin sakonnin ba gaskiya ba ne, mutane marar laifi da ka hallaka sun fika daraja a idanun jama’a da kuma Allah. Rayuwar ka ba za ta samu alfarmar Allah ba.
Asara na kawai ita ne hawayen da na zubar a kan rasuwar marigayin. Amma duk da haka, ina matuƙar farin ciki domin ya kare ne a cikin masallaci a inda ya ke bautawa Allah kuma ya kazance da azumi a ranar Litinin da aka kai harin.
Akika munji zafin mutuwarsa, amma ina so in gaya muka cewa ba za ka iya dakatar da mu daga zuwa masallaci domin yin ibada kuma ba za ka iya hana mu daga neman ilmi addini da kuma na zamani.
Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa
http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng