Ikon Allah! Ayoyin Al-Kur’ani sun bayyana a jikin jariri ( Hotuna)
- An haifi wani jaririn a garin Dagestan da rubutun ayoyin Kur’ani a jikinshi
- Mutane sunce wannan babban karama ce
- Mutane daga sassan kasar Rasha suna zuwa Dagestan domin ganin jaririn
Wani jaririn da aka haifa a shekarar 2009 a yankin Dagestan, kasar Rasha, ya janyo hankulan mutane daga sassan kasar daban-daban domin zuwa ganin ikon Allah yayinda ayoyn Al-Kur’ani mai girma sun bayyana a jikinshi.
Lokacin da ya kai makonni 2 da haihuwan jaririn mai suna Ali Yakubov, jikinsa ta fara bayyana ayoyin, wanda ke tafiya kuma ya sake dawowa bayan kwanaki. Ayoyin na rubuce da kalan yashi a fuskarshi, hannunsa, bayansa, da kafafuwarsa. Ana iya gani karara rubutun “Ka godewa Allah” a kafarsa ta dama.
Sagid Murtazaliyev, shugaban yankin Kizlyar,wanda ke arewacin birnin Dagestan, Makhachkala, yace “ faruwan wannan karama ta Allah na nuna mana cewa mu shugabanci kuma mu taimakawa yan uwanmu da samun zaman lafiya.” Wannan yankin ne aka fara musulunci a kasar Rasha.
Dagestan nada adadin mutane miliyan 3 masu kabilu guda 30.
Mutane kimanin 2,000 suna kawo ziyara a gidan iyayen Ali Yakubov, da ke cikin garin Kizlyar.
A yanzu dai, Ana boye Ali daga bainar jama’a kafin wasu su fara bauta mishi. A yanzu dai, wani attajiri ya ginawa iyayensa gidan kansu.
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng