Soja ya lallasa wani dan achaba har lahira a Legas

Soja ya lallasa wani dan achaba har lahira a Legas

Wani soja Najeriya majiyi karfu mai suna Sergeant Taiwo,ya yima wani dan babur mai suna Abu Alhaji dukan kawo wuka wanda ya tafi barzahu sanadiyarta.

Soja ya lallasa wani dan achaba har lahira a Legas
Soja ya lallasa wani dan achaba har lahira a Legas

A yanzu,Taiwo wanda aka fi sani da SirT mazaunin barikin Myyong,Yaba,kuma yana tsare yanzu.

Dan babur dinya dauki wata mata ne wacce ke son siyan kayan dadi cikin wani shagon cin abinci a Morroco, unguwar Shomolu, inda sojan ya ajiye motarsa Toyota Camry a wurin.

Jaridar Punch metro ta bada rahoton cewa yayinda Abu ya sauraron matan ta gama siyayyenta domin su cigaba da tafiya, Soja Taiwo wanda ya shiga mashaya a gaban gidan abincin ya fito domin daukan motarsa.

KU KARANTA: Amarya ta mutum jim kadan bayan aurenta

An samu cewa yayinda Taiwo ya shiga motarsa yayi ribas, motarsa ta bige babur din Abu Alhaji.

Wani idon shaida mai suna , Bolaji Oke , yace matar ta daki motan sojan domin nuna masa cewa ya bige mai babur kuma kada ya bige shi.

Sojan ya fito daga motarsa ya fara marin dan babur din. Yayinda Abu ke kokarin bayanin abinda ya faru, sojan ya fara dukan shi sosai fasinjan sai ta gudu.”

“Sojan ya dake sa har ya kasa tashi daga inda yake, shi kuma ya shiga motarsa ya tafi. Mutanen da ke wurin na tsoron sa baki saboda soja ne. wani ya fadawa kaninsa,wanda ya tafi wurin da wuri. An kai karan wannan abu bariki kuma an kaishi asibitin soji da ke Yaba misalin karfe 9 na dare,”.

Ance an kai karan wanna abu ofishin yan sandan Alade.

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng