Manyan illoli 5 da 'bilicin' ke jawowa, na biyu zai tsorata ku (Karanta)
-Hukumar NAFDAC ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina amfanin da man shafawan da ke dauke da sinadarin canja kalan fatar mutum wato Mecury da Hydroquinone.
-Hukumar tace duk man da ya kunshi yawan Mercury da Hydroquinone da ya wuce kashi 2 bisa 100 ya kan iya kawo wa fatar mutum illa.
KU KARANTA: Shugaban hukumar NEMA ya shiga tsomomuwa
Babban jami’I a hukumarNAFDAC din mai suna Mullah-Dadi ne ya fadi hakan lokacin da Kamfanin dilancin labaran Najeriya ta yi hira da shi a jihar Kaduna.
Ya kuma fadi illolin da irin wannan kayan shafan ke kawo wa da suka hada da;
1. Bata gaban mace da namiji
2. Bata huhu da kuma kodar mutum
3. Hana jirajiran dasuke cikin uwayensu girma yadda ya kamata
4. Tana sanadiyyar kamuwa da cutar daji
5. Bata fatar mutum
Bayan haka ya shawarci ‘yan Najeriya da kada suyi amfani da irin wadannan kayan shafa ba tare da su sami izinin likita ba.
Ya kuma yi kira da rokon masana da masu safaran wadannan kayan shafa da su hada karfi da karfe domin ganin sun hana shigowa da irin wadannan kayan, sun hana amfani da su da kuma siyar wa mutane a kasuwanni da shagunan kasa Najeriya.
Daga karshe ya ce mutane su dinga duba kwanakin da magungunan za su kare amfani da kula da lambar rajistan hukumar NAFDAC da kuma sunayen sinadarin da aka hada wajen sarrafa man saboda hakan zai taimaka wajen rage yawan kamuwa da cuttutukar da mutane ke fama da shi musamman wanda ya shafi fatar jiki.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng