Batun turo mai daga kasar Nijar zuwa matatan mai na Kaduna ta kankama
A wata ganawa data gudana tsakanin ministan harkokin man fetur da iskar gas na kasar Nijar, Mista Foumakoye Gado da shugaban kamfanin matatan mai ta Najeriya (NNPC) Alhaji Mai Kanti Baru, sun tattauna batun shirin da Najeriya ked a shin a samun man fetur daga kasar Nijar zuwa matatan main a Kaduna.
Ayarin tawagar da suka wakilici kasar Nijar a tattaunawar sun kai ziyarar aiki ne ga shelkwatar NNPC dake Abuja karkashin jagorancin jakadan kasar Nijar a Najeriya Mansour Mamman Hadj Daddo.
KU KARANTA:Boko Haram sun kashe wani dalibin jami’ar Maiduguri
Dayake dai ba’a bayyana cikakken bayanin batutuwan da bangarorin biyu suka tattauna ba, amma zaton tattaunawar bata rasa alaka dangane da shirin gwamnatin Najeriya na siyo mai daga kasar Nijar, wanda za’a turo zuwa matatan main a Kaduna.
A shekarar data gabata ne shugaban NNPC Maikanti Baru ya bayyana wannan shiri na gwamnatin tarayya, inda yace zata gina bututun mai mai tsawon sama da kilomita 1000 daga garin Agadem don turo mai zuwa matatan mai dake Kaduna.
NNPC tace ya zama wajibi ta fara neman sabbin hanyoyin samar da mai saboda yawan fama da matsalar fasa bututun maid a tsagerun Neja Delta ke yi, wanda hakan ke kawao tsaiko ga aikace aikacen matatan na Kaduna.
Wannan ya sanya aka fara tattaunawa tsakanin gwamnati da kasar Nijar da kasar Sin masu kulawa da rijiyoyin man kasar Nijar dake Agadem.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng